‘Malamai 70 sun bar jami’ar Maiduguri saboda Boko Haram’

Kungiyar malaman jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno a Najeriya, ta ce daga 2009 kawo yanzu malaman jami'ar guda 70 ne suka bar jami'ar sanadiyar ricikin Boko Haram.

Mai magana da yawun kungiyar, Dr. Danny Mamman ya ce rashin tabbas da rikicin na Boko Haram ya haifar ne ya janyo malaman suka bar jami’ar.

Sai dai kuma ya ce duk da rikicin na Boko Haram har yanzu akwai mutanen da ke neman aiki a jami’ar sannan kuma dalibai ba na zuwa karatu jami’ar.

Shi ma mai magana da yawun jami’ar ta Maiduguri, Farfesa Gambo Danjuma, ya ce “Tabbas lokacin da rikicin Boko Haram ya yi kamari wasu malamai da ma’aikata sun nemi su je hutu kuma sun dawo.”

Ya kuma kara da cewa “Ko a shekaran jiya sai da wasu masu neman koyarwa a jami’ar suka mika takardunsu.”

A watan Oktoba ne dai jami’ar ta Maiduri za ta koma daga hutun da ta ke yi.

A baya-bayan nan ne dai ‘yan kungiyar Boko Haram suka kashe ma’aikatan jami’ar guda biyar, yayin wani samame da suka kai wa wata tawagar ma’aiakatan hako mai a yankin arewa maso gabashin kasar.

Bayan nan kuma ‘yan kungiyar suka fito da wani bidiyo da ke nuna ma’aikatan jami’ar guda uku da suka yi garkuwa da su.

Har wa yau,ma’aikacin jami’ar guda daya ya yi batan dabo ba a gan shi ba.

Yawan hare-hare da Boko Haram ke kai wa jami’ar dai ya sanya ta kokarin shingace farfajiyarta.

Asalin Labari:

BBC Hausa

643total visits,2visits today


Karanta:  Za A Sabunta Wa’adin Kama Shekau

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.