Manoman Najeriya Na Son a Haramta Shigo Da Masara

Wasu Kungiyoyin manoma a Najeriya sun bukaci gwamnatin kasar da ta haramta shigar da masara a cikin kasar domin ganin an karfafawa manoman da ke samar da abinci.

Jagoran kungiyar Redson Tedheke ya ce shigar da masarar Najeriya zai zama zagon kasa ga shirin gwamnati na dogaro da kai da kuma ganin manoman sun samar da abincin da kasar ke bukata.

Sakataren tsare-tsare na kungiyar manoman Najeriya, Alhaji Muhammadu Magaji ya shaidawa RFI Hausa cewa an dauki matakin shigo da shinkafar ne domin gurgunta manoman arewa.

A cewarsa babu yadda gwamnati za ta ce mutane su rungumi noma kuma ta koma tana shigo da abincin da ake nomawa daga wata kasa.

Rahotanni sun ce Najeriya ta shigo da masara daga Brazil kusan ton dubu saba’in a tashoshin ruwan Lagos da Fatakwal.

Manoma na fargabar shigo da masarar daga waje zai karya farashin ta gida da ake nomawa, a yayin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke ikirarin farfado da sha’anin noma domin rage dogaro da arzikin fetir.

Asalin Labari:

RFI Hausa

517total visits,1visits today


Karanta:  An kama bindigogi sama da dubu daya a Lagos

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.