Masu Gangamin “Mumu don Do” Na Neman A Dawo da Tsohuwar Ministan Man Fetur daga Ingila

Biyo bayan irin makudan kudin da aka ce an gano tsohuwar ministar man fetur Alison Madueke ta wawure daga kamfanin NNPC masu gangamin "mumu don do" sun bukaci hukumar EFCC ta dawo da ita daga Ingila

Mabiya gangamin na Charlie Boy da ake yiwa lakabin “Our Mumu Don Do” sun gudanar da wata zanga zanga a Abuja yau saboda neman hukumar EFCC ta dauki matakan dawo da tsohuwar ministar man fetur daga Ingila inda nan ma an zargeta da wawurare kudade mallakar gwamnatin Najeriya.

Kasa da makonni biyu ke nan da suka gabata da ayarin Charlie Boy gudanar da zanga zanga makamancin na yau akan lallai Shugaba Buhari ya dawo gida Naijeriya ko ya yi murabus.

Masu zanga zangar sunyi anfani da ‘yancin da dimokradiya ya basu kuma sun ci nasara.

Dawowar shugaban kasa ta karfafawa ‘yan Charlie Boy karfin gwuiwa wajen gudanar da zanga zangar yau domin a dawo da Alison Madueke gida Najeriya ta fuskanci shari’a.

Asalin Labari:

VOA Hausa

488total visits,4visits today


Karanta:  Maigirma Alkali Tabbas Ni Mai Laifi Ne, Inji Evans

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.