Matar Da Aka Sace Da ‘Yarta A Sokoto An Same Su A Kaduna

Lokaci ne na jimami ga iyalan wata matar aure mai shekaru 26, mai suna Sa’adatu Umar Abubakar, inda ranar Litinin 4 ga watan Satumbar shekarar da muke ciki ta 2017 aka sace matar da ‘yarta a Sokoto kan hanyar su ta zuwa bikin radin suna a gidan wasu ‘yan uwansu dake cikin garin na Sokoto.

Majiyar mu ta fahimci cewa lokacin data bar gidanata dake unguwar Gidan Kanawa cikin Karamar Humumar Sokoto ta Kudu zuwa unguwar Gandu don halatar bikin, taji a jikinta cewa abubuwa basa tafiya dai dai.

Kamar yadda mijin matar Umar Abubakar mai shekaru 38 ya bayyana yanayinta ya canza tun kafin ta bar gidan a ranar da lamarin ya faru. Kai tun kafin nan ma, sai da ta dauki tsahon lokaci kafin ta bar kan gadonta duk kasala ta rufe ta kafin daga karshe ta tafi bandaki tayi wanka ta shirya don tafiya gurin bikin.

Da misalin karfe 2:30 na yamma aka lura cewa Sa’adatu da ‘yar tata sun bar gida don halartar bikin  kusada Babbar Kasuwar Cikin Garin na Sokoto.

“Kafin ta bar gida, sai da nayi mata addu’ar Allah ya kiyaye hanya,” a cewar mijin nata.

Amma lokacin da dare yayi babu su babu alamunsu, sai tsoro ya kamani.

Mijin ya kara dacewa “Na lura da wani abu mai ban mamaki inda matata da ‘yata basu dawo gida ba har goman dare. Nayita kokarin kiran wayarta sau da dama amma wayar bata shiga, daga nan na tafi gidan bikin wajen ‘yan uwana da ‘yan uwanta don bincika, amma babu labarinta”.

Karanta:  Boko Haram ta sace masu bincike na NNPC goma

“Daga nan muka dunguma muka tafi kafafen yada labarai inda muka bada sanarwar batan su. Mun kuma duba asibitoci, da caji ofis din ‘yan sanda dake  Kwanni dama cajin ofis din babbar kasuwar, yayin da dare ya raba sai muka yanke kauna.”

A cewarsa daga nan ne ‘yan uwa suka dukufa addu’a

“Muka kwana muna addu’a a masallaci inda mutane suka rinka karatun Al’kur’ani mai girma ana Addu’ar Allah ya bayyanasu,” a ta bakinsa.

Majiyar Daily trust bata samu jin ta bakin Sa’adatu ba don kuwa cewa akayi kanta na ciwo ba asan a dameta, amma ‘yarta ta wadda tare aka sace su ta yi karin haske kan abin da ya faru.

“Lokacin da muka ga yakamata mu koma gida, sai muka bar gurin bikin muka kama hanya inda babata ta tsayar da babur mai kafa uku. Akwai mai tuka babur din da kuma dan rakiyarsa a gaba sai kuma wata mata ita kade a baya tana zaune. Muna shiga cikin babur din sai duka muka rasa a ina muke, kawai sai tsintar kanmu mukayi a cikin wani daki tare da wasu mata uku, daya daga cikin matan daga gani ita ce maidakin,” a cewar yarinyar.

Daga baya ne suka lura cewa ashe a garin Kafachan na Jihar Kaduna suke.

Yarinyar ta kara da cewa: “Akwai mutane da dama dake shige da fice a gidan, haka kuma suna wani yaren da ni bana gane me suke cewa. Ni da mahaifiyata mun kasance a wannan dakin tare da wasu mata biyu, tsahon zaman mu ana ciyar damu taliyar ‘yan yara ne kawai sau uku a rana.”

Karanta:  An sace gwamman mutane a Kaduna

A cewarta, mahaifiyarta taki cin abinci duk lokacin da aka kawo, inda ta dukufa addu’a ba kakkautawa.

“Taki yin bacci amma ni kuwa na kan danyi bacci jifa jifa,” a cewarta.

Rumasa’u tace sun shafe kwana 2 a tsare a rana ta uku kuwa karar harbe-harbe ce daga wajen gidan ta firgita su inda duk mutanen dake gidan suka fice daga cikin gidan a guje.

“A lokacin da muka fito a guje daga cikin gidan ne wani soja ya rike hannun mahaifiyata ya shigo damu cikin motarsu. Suka kaimu gidansu daga nan ne Kawunnena suka dauko mu zuwa gida Sokoto,” a cewarta

Abubakar yace lokacin da matar tasa da ‘yarsa suna tsare cigaba sukayi da addu’a babu kakkautawa har tsahon kwana biyu har ranar Laraba 6 ga watan Satumba, da misalin karfe 2 na yamma daya daga cikin dangin matar tasa ya kirashi ta waya ya sheda masa cewa an sami matarsa a wani gida a Kafanchan, a jihar Kaduna amma tana cikin kulawar jami’an tsaro kuma tana nan kalau

“Sai duka mutanen dake wannan gurin suka dau murna, suna godiya ga Allah wanda cikin rahamarsa ya amsa addu’arsu,” a ta bakinsa.

“’Yan uwanta su tafi Kafanchan suka taho da ita gida. Nayi mutukar farin cikin dawowarsu gida lafiya. Na barta ta kwana da iyayenta domin ta samu hutu. Na tafi gurinta kashegari  amma saboda tururuwar da mutane keyi cikin gidan nasu bamu samu ganawa a kadaice ba sai dai nan gaba,” a cewarsa.

Yace yanada yakinin cewa zasu dawo gida ganin irin mutanen da suka taimaka wajen gudanar da addu’o’i.

“Na san cewa irin wadannan mutanen Allah bazai taba watsa musu kasa a ido ba idan suka roki wani abu a gurinsa. Abubakar ya bayyana matar tasa da cewa mai tsoron Allah ce, gata da saukin kai da kuma biyayya.

Karanta:  NDLEA ta kama kilogaram 881.100 na kwayoyi a Sokoto

“Takanyi duk abun da zata iya don ta faranta min, abokiyar zama ce ta gari wadda ta cancanci a zauna da ita,” a cewarsa.

Dangane da ‘yan uwa, makota da abokan arzikin Sa’adatu kuwa abun ba a cewa komai domin idan ka kalli hasken farin cikin fuskokinsu da yadda suke magana cikin farin ciki lokacin da sukaji labarin cewa anga mahaifiyar da ‘yarta  cikin koshin lafiya.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

2694total visits,3visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.