Matar Da Tafi Kowa Shekaru A Duniya Ta Mutu A Jamaica

Matar da tafi kowa shekaru a duniya Violet Brown ta mutu a Jamaica tana da shekaru 117 da kwanaki 189 a duniya.

Firaministan Jamaica Andrew Holness shi ya bayyana ta’azziyarsa a shafinsa na Facebook, inda ya kira ta da cewa “Mace wadda ta taka rawar gani kuma abar koyi”

Matar wadda aka sani da suna “Aunt V” ta mutu ranar Jumma’a a wani karamin asibiti inda ake kulawa da ita kan ciwon bugawar zuciya da karancin ruwa a jiki

Da mutuwar matar ne Kungiyar Masu Bincike kan Mutanen da suka fi dadewa a Duniya suka bada sunan Nabi Tajima ‘yar kasar Japan a matsayin matar da tafi kowa yawan shekaru a duniya. An haife ta ranar 4 ga watan Agusta ta shekarar 1900.

Brown ta tafiyar da daukacin rayuwarta lokacin tana raye gun yankan rake. Haka nan mace ce mai kokari sosai a Coci in banda ‘yan kwanakin nan, hazika ce wadda ta maida hankali sosai kan addininta na Kiristanci.

Tana da ‘ya’ya maza hudu mata 2. Babban danta ya mutu a watan Afirilu yanada shekaru 97 a duniya. (NAN)

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

645total visits,1visits today


Karanta:  Hana daukar waya yayin tsallaka titi a Amurka na tayar da kura

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.