Matasan Katsina sun nesanta kansu da kalaman Sarkin Katsina kan Inyamurai

Haddadiyar Kungiyar ci gaban matasa ta Katsina, ta kara jadadda cewar sanarwar 1 ga watan Oktoba da aka bawa kabilar Inyamurai tana nan daram dam duk da cewar Mai Martaba sarki Abdulmumin Usman na kabilar Ibo da su zauna a Arewa kar su tafi ko’ina.

Babban Sakatare na kungiyar, Abdullahi Marusa ta sanar da hakan a wajen wani babban taro da aka yi da manema labarai sa’a 24 bayan da Mai Martaba ya tabbatarwa da Inyamurai matsayinsa. Kungiyar ta yi bayanin cewar, suna ganin girma da martabar Sarki, amma babu gudu ba ja da baya kan matsayar da aka dauka ta 1 ga Oktoba.

“Sakacin da aka yi na barin Nnamdi Kanu wajen wasa da hadin kai da zaman lafiyar kasa abin dubawa ne, kasancewar wannan yanki ya yi shiru na tsawon lokaci duk da wannan fitsara da suke aikatawa”.

“Wasu daga cikin ‘yan Arewa kamar Atiku da Bugaje sun fito karara sun nuna kansu a matsayin wadanda ba sa kishin Arewa, wadannan mutane kiris suke nema domin amfanuwa da irin wannan hargowa” – inji Abdullahi Marusa.

 

Asalin Labari:

DailyTrust, Muryar Arewa

1808total visits,1visits today


Karanta:  Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kai 'Yan IPOB 67 Kurkuku

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.