Matata Da ‘Ya’yana 5 na Hannun Boko Haram

Wasu da iyalansu ke hannun mayakan Boko Haram na cigaba da bayyana halin damuwar da suke ciki, a dai dai lokacin da hukumomin Najeria ke ikirarin samun nasara a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.

Editan BBC na Abuja, Naziru Mikailu ya yi kicibis da wani mutumin garin Bama dake jihar Borno, wanda yanzu yake Abuja, kuma wanda mayakan Boko Haram suka sace matarsa da ‘ya’yansa biyar, a cikin shekaru 4 da suka gabata.

Ya dai nemi sakaya sunansa saboda matsalar tsaro.

Ya fara da bayyana makasudin dalilin barin gidansa da garinsa a lokacin da rikicin Boko Haram ya isa garin na Bama:

“A da muna cikin garin Bama ne. To, da abin ya dau wuta, sai muka gudun hijira zuwa Kamaru ni da iyalina biyu da ‘ya’yana goma”.

Ya ce daga baya ya dawo gida daga Kamaru, kuma ya aika wa iyalan nasa kudi domin su dawo.

“Daya ta sami fitowa daga Kamarun zuwa Bama, amma dayar an riketa da ‘ya’yanta biyar”, inji mutumin.

Yace: “zai kai shekara uku zuwa hudu da faruwar wannan abun. Sam ban sake jin labarinsu ba, kuma ban san inda suke ba”.

Ya ce saboda matsalar ta yaki da Boko Haram, ya kasa komawa ya nemo iyalin nasa a wancan lokacin.

“Ina da niyyar in tafi in duba su, amma ba halin tafiya. Ba hanyam babu halin tafiya”.

“Ni da kaina ina kwana biyu ko uku bana iya barci saboda zulumi. kuma idan na tuna da su ma ba na iya cin abinci ma”.

Ya ce har yanzu bai sanar da sauran ‘ya’yansa halin da ‘yan uwan nasu dake hannun mayakan Boko Haram gaskiyar al’amarin ba:

“Ina gaya musu ‘yan uwansu basu sami tahowa ba, suna can a Kamaru. Idan na sami kudi zan aika musu domin su dawo”.

Karanta:  Gwamnonin arewa za su ba Borno tallafin N360m

Ya sanar da BBC cewa duk da halin da yake ciki, bai sanar da hukumomi cewa mayakan Boko Haram na rike da matrsa daya tare da ‘ya’ya biyar ba, amma yana da karfin zuciyar cewa iyalinsa suna nan raye, kuma wata rana zasu hadu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

938total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.