Matata Tayi Barazanar Kona Ni, Miji Ya Shaidawa Kotu

Wata kotun Majistire a garin Ibadan ranar talata ta raba auren Akibu Oyewole da matarsa Omolara. Kotun ta raba auren mai kusan shekarau 8 sakamakon barazanar da matar tayi na hallaka maigidan nata.

Da yake yanke hukunci shugaban kotun Mr Ademola Odunade ya bada kolawar yaran ma’auratan biyu ga Omolara inda kuma kotun ta ummarci Akibu da ya ringa biyan N8,000 duk wata kudin kulawa da yaran.

 

Odunade ya kara ummarta mai karar da xaukar dauniyar karatun yaran dama walwalarsu

Akibu dai Dan Acahaba ne, inda yake cewa matar tasa ta yi yinqurin babbake shi tare da yaran nasu.

” Shugabana, ban tava ganin tashin hankali a rayuwa taba kamar wannnan mata tawa Omolara.

“Saboda rashin san zaman lafiyarta da shaidancinta, shekara biyu bata gidana, haka na hakura na sake aurenta.

“Duk da cewa ‘yan uwan sun soki lamari na mayarda da auren, amma nayi kunnen uwar shegu

“lokacin da zata tafi, sai ta tattare kayana ta tafi da su.

“Jim kadan da dawowarta, Maigirma, sai ta ci gaba da mummunar hallin nata kamar yadda ta saba yayin da rufe qofa, ta xaukko wuqa mai kaifi da gallon xin  fetur tana barazanar qona ni da yaran tare da ita bakixaya.

“ babu abinda zan iya don kuvutar da kai na da yaran kafin Allah ya kawo mana xauki.

“Na gaji da munana xabi’un Omolara, don Allah a raba auren mu”

Amma Omolara wadda itama ta yadda a raba auren ta shaidawa kotun cewa tsorata mijin nata Akibu kawai take yi

“Maigirma Alkali bana nufin barazanar rayuwarsa da ta yaran.

Karanta:  Priyanka Chopra Da Rahama Sadau Zasu Gana

“Yanzu nasan cewa babu wata soyayya a tsakaninmu” in ji Omolara

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

337total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.