‘Mazan’ da suka yi wa wata mata fyade sun watsa mata Acid

Ana zargin maza biyun da suka yi wa wata mata fyade da watsa mata sinadarin acid, bayan da aka bayar da belinsu.

‘Yan sanda sun ce ta zargi mutane biyun ne da wani mutum da ba ta ganeshi ba da watsa mata sinadarin acid ranar Litinin, bayan da ta ki amincewa da yin watsi da shari’ar da ake yi da su.

A watan Mayu ne suka yi mata fyaden a birnin Farrukhabad da ke jihar Uttar Pradesh a arewacin Indiya. Mutum uku aka tsare a kan laifin, inda har yanzu daya daga cikinsu yake tsare.

Tuni ‘Yan sandan suka kaddamar da samame don kamo biyun da ake zargi.

An kai wa matar harin ne a lokacin da take dawowa daga wata karamar kotu, don kalubalantar belin da aka bayar na mutum biyun da ake tuhuma.

Wani sufuritandan ‘yan sandan ya shaida wa BBC cewa, ana zargin wadanda ake tuhuma ne suka dauki matar suka kai wani boyayyen wuri kuma suka bukaci ta yi watsi da karar.

Ya kara da cewa, “Ta yi korafin cewa sun watsa mata sinadarin acid a fuskarta bayan da ta ki amincewa”.

An bayar da rahoton cewa ta samu mummunan rauni a fuskarta da jikinta, yanzu haka kuma ana kula da ita a wani karamin asibiti.

Bincike a kan rikicin fyade a Indiya na karuwa tun lokacin da wasu gungun mutane suka yi wa wata fyade da kuma kashe wata daliba a motar bas a birnin Delhi.

Sai dai kuma, ana dada ci gaba da samun rahotanni a kan yi wa mata da kananan yara fyade a fadin kasar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

371total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.