MDD ta Gargadi Venezuela Kan Take Hakkin Bil’adama

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa karuwar take hakkokin bil’adama a Venezuela na kawo nakasu ga Demokradiyyar kasar. Gargadin Majalisar Dinkin Duniyar dai na zuwa ne a dai dai lokacin da sabuwar majalisar dokokin kasar ke sanar da fara tuhumar jagororin adawar kasar kan cin amanar kasa.

Majalisar wadda ta sanar da amincewa da dokar da wadda za ta fara tuhumar jagororin adawar a yau Laraba, ta ce hakan zai kawo karshen mara bayan da jagororin adawar ke yi ga takunkumin Amurka kan kasar.

Duk da cewa, bayanai dangane da sabuwar dokar basu fito karara sun fayyace jagororin adawar da Majalisar za ta tuhuma ba, amma mambobin Majalisar na zargin shugaban Majalisar wakilan kasar Julio Borges da mataimakinsa Freddy Guevara.

A cewar wata ‘yar majalisa Iris Varela, suna da tabbacin cewa dokar za ta bi takan mutane biyun don zartas musu da hukunci kana bin da suka tafka.

Ko a juma’ar makon daya gabata ma dai Amurka ta kara kakabawa Venezuela wasu sabbin takunkumai wanda Rasha ta kira da yunkuri rugurguza tattalin arzikin kasar tare kuma da haddasa rikici.

Shugaba Nicholas Maduro dai na zargin bangarorin adawar da rura wutar data kai ga kara sabbin takunkuman wanda ya ce sabuwar dokar ce zata magance matsalar.

Bisa ga tanadin dokokin Venezuela, akan yankewa wanda aka samu da laifin cin amanar kasa hukuncin daurin shekaru 20 zuwa 30 a gidan yari.

A cewar bangaren adawar kasar dai yanzu haka akwai Fursunonin siyasa kimanin 590 a kasar ta Venezuela.

A baya bayan nan ne dai wata zanga-zanga da masu adawa da shugabancin Maduro suka jagoranta kan halin da kasar ke ciki na matsin tattalin arziki ta yi sanadin mutuwar kimanin mutum 125, wanda kuma aka yi zargin cewa galibinsu sun mutu ne a hannun jami’an gwamnatin kasar.

Asalin Labari:

RFI Hausa

548total visits,3visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.