Me Ake Ciki Game Da Cutar Zika Yanzu A Duniya

Masu Ilimin kimiyya suna kara gano sababbin bayanai game da kwayar cutar Zika kusan kowacce rana.

Masu Ilimin kimiyya suna kara gano sababbin bayanai game da kwayar cutar Zika kusan kowacce rana. Kuma abinda suke ganowa yana kara tada hankali. Wakiliyar Muryar Amurka Carol Pearson ta ruwaito cewa, babu wani abinda yake da dama dama dangane da kwayar cutar Zika ko kuma Sauron dake yada ta.

Tun lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana kwayar cutar Zika, a matsayin cutar dake bukatar daukar matakin gaggawa, masu ilimin kimiyya suke danganta cutar da shanyewar gababuwan jiki da kuma cututukan kwakwalwa tsakanin wadanda suka manyanta, sai dai kwayar cutar tafi illa ga jarirai dake girma a ciki.

Wani nazari da aka gudanar cibiyar aikin jinya ta John Hopkins dake birnin Baltimore a Amurka ya nuna cewa kwayar cutar Zika tana kamawa ta kuma kashe kowanne karamin kwai na naman jiki da zarar ya kunno kai a kwakwalwar jariri lokacin da take girma.

Wani binciken da aka yi kan mata masu ciki a kasar Brazail, ya nuna kimanin kashi ishirin da tara cikin dari na jariran dake girma a cikinsu suna dauke da kwayar cutar Zika.

Dr Anthony Fauci na cibiyar nazarin kiwon lafiya yace adadin yana da tada hankali. “Mun hakikanta cewa, akwai kananan matsaloli ko nakasa da ba za a iya ganewa ba ta irin wadannan gwaje-gwajen, saboda haka, ina tsammani illar da kwayar cutar take yi ga jariran dake girma a ciki ta shige kashi ishirin da tara cikin dari.”

Nakasar ta hada da rashin gani da kyau, kurmanci, rashin kwakwalwa-dakikanci da kuma illoli da zasu shafi jarirai da za a ga kamar lafiyayyu ne.

Karanta:  Cutar da ba a Sani ba ta Kashe Mutum 62 a Nigeria

Sai dai kusan sai kace shawarar da ya bayar bata sanyaya zukatan mata matalauta dake kasashen kudancin Amurka da kuma Caribbean ba.

“Kada ku bari cutar ta kamaku, Kuyi rigakafi domin magance kamuwa da cutar. Wannan ce hanyar da tafi dacewa, ta maganin makuwa da cutar.”

Sai dai yanzu haka, cutar bata da rigakafi. Kuma ko da yake ana kan kokarin samar da rigakafin cikin sauri, zai dauki shekaru biyu ko uku kafin ya samu. Hanya daya kawai ta kare kamuwa da cutar ita ce sa dogon wando da taguwa mai dogon hannu, da kuma amfani da gidan sauro, da maganin sauro da zai kashe sauro da kwayayenshi.

Wata matsala kuma ita ce kudi. Majalisar Amurka bata riga ta tanada karin kudi da za a ci gaba da bincike ba. Idan ba tare a kudi ba, aikin zai ja da baya ko kuma ya tsaya baki daya.

 

Wani kididdiga da wata cibiyar dake aikin kokarin kawar da cutar ta cutar daji a nahiyar Afrika mai suna Partnership for Eradication of Cancer in Africa ta fitar ya nuna cewa a duk shekara akwai kimamin mata dubu goma sha hudu da tamanin da tara da suke kamuwa da cutar daji ta bakin mahaifa, daya daga cikin cututtukan daji da take illa ga mata.

Kungiyar Lafiya ta duniya tace cancer bakin mahaifa itace cuta ta biyu dake kama mata, yan tsakanin shekaru goma sha biyar zuwa arba’in da hudu a Nigeria.

A hira da wakilin sashen Hausa Babangida Jibirin yayi da Dr Mohammed Mohammed. Dr Mohammed yayi bayanin cewa cancer kan fito ne kamar kurji ko kumburi, yawancinsu, amma ba wai dukka dole sai ya zama kumburi ba.

Karanta:  Ana bincike ko cutar kyandar birrai ta je Kano

Yace cancer ba kamar sauran cututtuka ba, maimakon ya daina toho, sai yayi ta toho, harma ya hana wasu sashen jiki yin aiki yadda ya kamata.

Dr Mohammed yace idan aka tare tsirowan yana fitowa, to ana iya samun nasarar warkar da shi, in ba haka ba idan ya kai wani mataki, to sai gyaran Allah domin da wuya a iya warkarwa.

 

Asalin Labari:

Muryar Amurka

847total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.