Me Marubutan Nigeria Keyi a Lebanon?

A yanzu haka wasu marubuta goma daga sassa daban-daban na Najeriya na ziyara a kasar Lebanon a karkashin wani shiri na karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu ta fuskar adabi.

Marubutan na halartar tarurrukan bita suna kuma ziyartar wuraren tarihi da nufin kara fahimtar alakar da ke tsakanin al’ummun duniya ta fuskar al’adu.

Gidauniyar Wole Soyinka ce ta shirya shirin da hadin gwiwar Cibiyar Cedars ta kasar Lebanon da kuma Jami’ar Notre Dame ita ma ta Lebanon.

A wannan hira da ya yi da Muhammad Kabir Muhammad, daya daga cikin marubutan, wanda kuma malamin makaranta ne a Kano, Khalid Imam, ya yi bayani a kan alfanun shirin.

Khalid Imam: Kamar yadda shugaban cibiyar Cedars ya tabbatar mana, a tsakanin Najeriya da kasar Lebanon akwai tsohuwar dangantaka wadda ta kwashe shekaru masu yawa.

Amma kuma dangataka ce wadda ta fi karfi ta bangare daya, wato bangaren kasuwanci. Sai suka ga ya kamata su bijiro da wani tunani wanda ta harkar ilimi, ta harkar rubutuda sauran bangarori za a kyautata dangataka tsakanin kasar Najeriya da kasar Lebanon. Kuma ita wannan cibiya ta Wole Soyinka ta tattaro marubuta daga dukkan sassan Najeriya.

Tambaya: To amma me ya sa ba a zabi mutane daga wasu bangarori don a kulla wannan alaka ba, sai marubuta?

Khalid Imam: Ka san su marubuta ai kusan aiki iri daya suke yi da ‘yan jarida.

Tasirin abin da ake bukata shi ne, wannan wayar da kai da ake masu, to ya kasance kuma sun rubuta shi sun yada shi cikin al’umma don al’umma don al’umma su gane cewa ban da kasuwanci akwai sauran damammaki da mutane da su iya samu. Misali damammakin a je a karo ilimi, da aikin yi, da sauran irinsu.

Tambaya: To a matsayinka na marubuci, idan aka kammala wannan shiri, ta yayay kake ganin zai inganta rubuce-rubucenka?

Karanta:  Ganduje ya debi ma'aikatan lafiya 2,458 a Kano

Khalid Imam: Yanzu ma kafin in taho mun fara wasu maganganu wadanda suka shafi bunkasa harkar rubutu.

Kuma mun kai ziyara wani daki na bude ido wanda aka gabatar da shi don tunawa da wani mashahurin marubuci na kasar Lebanon wanda ake cewa Khalil Gibran, kuma masu kula da wurin sun yi murna cewa an fassara rubutun shi wannan marubuci na kasar Lebanon a cikin harsunan duniya masu yawa; suka ce to ga Najeriya babbar kasa ce amma ba a fassara rubutunsa a harsunan ta ba.

Har yanzu sun fara maganar cewa za a samu ‘yan Najeriya su fassara littafin shi wannan mashahurin marubuci a cikin harshen Hausa, da harshen Yarbanci, da harshen Ibo.

Kuma har sun fara karfafa cewa da Hausa za su fara bisa bayanin da na yi masu cewa Hausa ta fi ko wanne harshe a Najeriya yawa, da kuma rubutu wanda yake ya shafi adabi, domin tarihi ne wanda yake tsoho – al’ummar Hausawa wadanda suke arewacin Najeriya sun dade da farkawa da harkar rubutu tun kafin Turawan Yamma su zo.

Zancen nan da nake da kai ma mun fara magana da su cewa wajibi ne za su dubi yadda za su isar da sakonsu zuwa ga ofishin jakadancin Najeriya da yake nan Lebanon, domin a ga ta wanne bangare za a bullo da cewa wani daga Najeriya ya zo nan Lebanon, ya fassara aikin wannan mashahurin marubucin; sannan wani daga Lebanon ya je kamar misali Kano, a dauki wani babban marubuci kamar Mudi Sipikin, ko Mu’azu Hadejia, shi kuma a fassara rubutunsa daga harshen Hausa zuwa harshen Faransanci ko Larabcin Lebanon.

Karanta:  Kwankwaso ya Kauracewa Babban Taron APC a Kano

Tambaya: To da yake ka yi maganar cewa za a fassara littattafan shi wannan mashahurin marubuci na Lebanon zuwa harshen Hausa, wacce gudunmawa kake ganin hakan zai bayar wajen bunkasar harshen Hausa da kuma adabin Hausa, musamman?

Ka ga Hausa ai za ta kara bunkasa, za ta kara fadada a wasu sassan duniya da ba ta kai ba, misali kamar kasar Lebanon – babu rubutu a wuraren da muka je wadanda suke littattafai da aka yi da Hausa.

Kuma har sun fara tunanin a kawo dalibai ko marubuta wadanda za a yi irin abin da ake kira “exchange” – wasu su zo nan, wasu kuma su je can.

Ma’ana, kamar irin wannan zuwan namu, to kuma a debo dalibai wadanda za su karanci adabi na Lebanon, wasu kuma a debo daga Lebanon a kawo su misali Jami’ar Bayero (ta Kano) su kuma a koya masu adabin Hausa.

Malam Khalid Imam, daya daga cikin marubuta goma ‘yan Najeriya da ke halartar wani shirin musayar fasahar adabi a Lebanon.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1042total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.