Mene ne Shugaba Buhari Bai Fada Ba a Jawabinsa?

Yayin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa al'ummar Najeriya jawabi, akwai wasu manyan batutuwa da jama'ar kasar suke ganin ya dace shugaban ya tabo amma bai yi maganarsu ba.

Akwai masu ganin cewa jawabin shugaban ya fi mayar da hankali ne a kan mayar da martani ga masu fafutikar ballewa daga Najeriya.

Sai dai jawabin ya tabo batun tsaro musamman yaki da Boko Haram da satar mutane don neman kudin fansa da kuma rikicin Fulani makiyaya da manoma.

Har ila yau akwai al’amura da aka yi zaton cewa shugaban zai magana a kansu amma bai yi ba.

Batun lafiyarsa

Shugaba Buhari bai yi wa ‘yan kasar karin haske ba game da rashin lafiyarsa musamman batun cutar da ya yi fama da ita.

Ya bar ‘yan kasar cikin duhu game da tambayoyi kamar: Ko zai sake komawa duba lafiyarsa a nan kusa?

Mene ne sunan ciwon da ya yi fama da shi?

Ko ya samu umarnin likitocinsa kafin ya koma gida?

Haka zalika akwai wadanda suka tsammaci shugaban ya yi tsokaci a kan kokarin da gwamnatinsa take na ganin an gyara fannin kiwon lafiyar kasar wanda ga alama rashin tabbas kan hakan ne ya sa shi zuwa kasashen ketare neman magani.

A waccan karon da ya dawo jinya dai ya yi magana kan wadannan batutuwa.

Yakin da cin hanci da rashawa

Shugaban bai ce komai ba game da babban abin da ya yi suna wajen yaki da shi a kasar, wato cin hanci da karbar rashawa.

Musamman ganin yadda gabanin ya fara jinya sai da aka dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal don a bincikensa kan zargin karbar cin hanci.

Ga kuma batun Shugaban Hukumar yaki da yi wa tattalin arziki kasa ta’annati EFCC Ibrahim Magu wanda har yanzu majalisa ba ta amince ta tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar ba.

Karanta:  "An yi wa Fulani kisan-ƙare-dangi a Taraba"

Ko da dai ba a zaci ya yi jawabi mai tsawo kan batun Babachir da Magu ba, amma an sa rai zai yi magana kan ci gaba da yaki da cin hanci da rashawar da ya fara kafin ya je jinya.

Yajin aikin malaman jami’o’i

Shugaban bai ce komai ba game da yajin aikin malaman jami’o’in kasar wanda ya shiga mako na biyu.

Ayyukan ci gaban kasa

Batun ayyukan ci gaba da samar da wutar lantarki su ma ba sa cikin batutuwan da shugaban ya tabo a jawabin nasa.

Mataimakinsa Yemi Osinbajo

Hakazalika shugaban bai bayyana gamsuwarsa ko rashin gamsuwarsa game da rawar da Mataimakinsa Yemi Osinbajo ya taka yayin da yake jinya.

Mista Osinbajo ne ya rika tafiyar da kasar a matsayin mukaddashin shugaban kasa har tsawaon fiye da wata uku.

A wancan karon da ya dawo Shugaba Buhari ya yabawa mataimakin nasa kan yadda ya tafiyar da kasar, shi ya sa ma jama’a suka sa ran zai sake yin hakan a wannan karon.

Tattalin arziki

Wasu masana tattalin arziki a Najeriya sun nuna rashin jin dadi kan yadda Shugaba Muhammadu Buhari bai tabo batun tattalin arzikin kasar ba a jawabin nasa ba.

Malam Abubakar Aliyu masanin tattalin arziki ne a Najeriyar, ya kuma shaidawa BBC cewa abin bai mu su dadi ba, ganin Shugaba Buhari bai tabo wannan bangaren ba alhalin an samu ci gaba sosai musamman ta bangaren aikin noma, da ci gaban da masana’antu suka samu sakamakon kawo wasu sabbin tsare-tsare, da ko shakka babu sun taka muhimmiyar rawa wajen sanya su fara aiki gadan-gadan.

Karanta:  Boko Haram Ta Fitar Da Bidiyon Ma’aikatan Jami’ar Maiduguri Da Ta Yi Garkuwa Da Su

Malam Abubakar ya kara da cewa, da shugaba Buhari ya tabo batun tattalin arziki a jawabin da ya yi da safiyar Litinin ga ‘yan kasar, da kasuwar hannayen jari ta yi armashi, ma’ana hannayen jari za su yi daraja a kasuwar hada-hadarsu.

Ya kara da cewa rashin yin wani jawabi da ya shafi tattalin arziki, zai janyowa kasuwar koma baya ta inda hakan zai dasa tsoro a zukatan masu zuba jari su dan yi dari-dari, kafin su saki jiki, hakan kuma ba karamin koma baya ne ga dan tagomashin da wannan fannin ya fara samu.

Masanin tattalin arzikin ya ce, yanayin da aka ga Shugaba Buharin a jawabin nasa, yanayi ne da ke ba da kwarin gwiwa kan cewa ya samu lafiya komai zai ci gaba da gudana musamman tattalin arziki kamar yadda gwamnati ta sha nanatawa, to amma gwiwarsu ta yi sanyi da yanayin jawabin da sam babu wani abu da ya tabo a bangaren tattalin arziki.

Asalin Labari:

BBC Hausa

567total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.