Messi Yana Jan Kafa Wajen Sabunta Yarjejeniya Da Barcelona

Mai yiwuwa ne Lionel Messi ya raba gari da kungiyar Barcelona a karshen kakar wasa ta bana, ganin yadda dan wasan ke cigaba da jan kafa wajen rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya da kungiyar.

Majiyoyi kwarara sun rawaito cewa Messi mai shekaru 30,  har yanzu bai yanke hukunci na karshe ba, dangane da cigaba da zamansa a kungiyar ta Barcelona.

A cewar jaridar Daily Express da ake wallafawa a turai, wannan rashin tabbbas, da ke fuskantar Barcelona, ya biyo bayan gazawar kungiyar, wajen sayan Philippe Coutinho daga Liverpool da kuma Angel Di Maria daga PSG.

A watan da ya gabata ne dai kungiyar Manchester City, ta fara zawarcin Messi, wanda kuma tun a waccan lokacin wakilan kungiyar ta City suka fara tuntubar Messi bayan yi wa Barcelona tayin saye shi kan euro miliyan 275.

A gefe guda wasu na ganin kamata ya yi Messi ya sauya sheka zuwa ingila ko ma dai wata kasar, don a ga bajintarsa, inda ake muhawarar ko yana  daga cikin ajin ‘yan wasan da bayan sun canza kungiya tauraruwarsu zata yi kasa ko kuma zata daga.

Daga cikin misalan ‘yan wasan da suka sauya sheka kuma hakan bai yi musu kyawu ba, akwai Robinho da ya koma Manchester City daga Real Madrid, sai Andriy Shevchenko da ya koma Chelsea daga AC Milan, da kuma misalin Ricardo Kaka da taurarwarsa ta dusashe bayan komawa Madrid daga AC Milan.

Kadan daga ‘yan wasan da gaba ta kai su gaba, wai gobarar Titi a jos kuwa, akwai Ronaldo na Brazil da ya murza leda a Barcelona, Inter Milan da kuma Real Madrid ko ina kuma yayi bajinta, sai Zinaden Zidane ya taka rawar gani a Juventus ya koma Madrid ya kuma yi bajinta a can.

Asalin Labari:

RFI Hausa

1891total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.