Mijina Mashayin Giya Ne Don Haka A Raba Auren Mu, Wata Mata Ke Fadawa Kotu

Daga Ibadan – Shugaban wata Kotun Gargajiya dake Mapo a Ibadan Mr Ademola Odunade ranar Alhamis ya raba wani aure mai tsahon shekara 16 tsakanin Bunmi da mijinta Ayoola Makinwa saboda dalilin shan giya da rashin iya daukar nauyinta.

Da yake yanke hukunci, Odunade ya shawarci maza da mata dasu dukafa da addu’a lokacin da suke kokarin samawa kansu abokan zama saboda karsu fada mugun hannu.

Lokacin da take maida ba’asi Bunmi wadda ‘yar kasuwace cewa tayi mijin nata Ayoola dan giya ne kuma baya iya dauka nauyinta.

“Ayoola yafi maida hankali akan shan giya fiye da nauyin dake kansa na matsayin uba ga ‘ya’yansa da kuma matsayin miji ga matarsa.

“A magana ta gaskiya, yafi zama annoba ga ‘ya’yan nasa maimakon zama rahama garesu saboda yadda yake mana barazana da yunwa saboda ya kasa hana kansa ta’ammali da giya.

“Seda takai sauda dama ina hada inawa-inawa ina bar masa gidan saboda rashin iya tafiyar da rayuwar iyalinsa, amma mahaifiyata tayita shawartata da nayi hakurin zama dashi.

“Yanzu na gama fusata, bana kaunarsa ko kadan, tuni na bar masa gidan tsahon shekara daya da rabi,” Bunmi take maida jawabi. Duk da yake cewa Ayoola yaki amincewa da maganar matartasa na raba auren ya dai ki cewa komai dangani da zargin matartasa. “Maigirma Alkali, Bunmi batada hakuri saboda koyaushe idan abu kalilan ya ratsa tsaninmu, sai ta hada inata-inata ta barmin gidan, amma duk da haka ina sonta,” kamar yadda ya bayyana. Ma’auratan na zaune ne a Odinja ta garin Ibadan haka kuma Ayoola dan achaba ne.

Karanta:  Kotu Ta Amince Gwamnati Ta Rike Kudaden Diezani
Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

435total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.