Minista ya zabga wa wata mata mari a Afirka Ta Kudu

Ana zargin mataimakin ministan ilimi na Afirka Ta Kudu Mduduzi Manana, da dukan wata mata a yayin da wata hayaniya ta barke a mashaya.

Mista Manana dai har yanzu bai ce komai ba kan batun.

Sai dai a wata hira da aka nada, an ji wani mutum da aka yi amannar cewa ministan ne yana cewa tabbas ya mari matar.

Gwamnatin kasar dai ta ce taba sane da zargin da ake wa ministan.

Afirka Ta Kudu na daya daga cikin kasashen da ake yawan samun cin zarafin mata a duniya.

Alkaluman da ‘yan sanda suka fitar ya nuna cewa an samu laifuka 64,000 a shekarar da ta gabata.

Wani mai magana da yawun ‘yan sanda ya tabbatarwa kamfanin dillanci labarai na AFP cewa suna bincike kan lamarin da ya faru a ranar Lahadi.

Wani dan jaridar wata kafar yada labaran kasar, Lumko Jimlongo, ya ganewa idonsa abin da ya faru a mashayar Cubana da ke kusa da birnin Johannesburg.

Ya shaida wa kafar yafda labaran SABC cewa, wacce aka mara ta yi kokarin ta fita a lokacin da ta gigice, “sai ta fadi a kasa, sannan kuma ya bita ya taka mata kai da kafarsa”.

Ministan mata da ke ofishin shugaban kasar, Susan Shabangu, ta yi Allah-wadai da zargin da ake wa mataimakin ministan.

A wani bayani da ta yi ta kara da cewa, “ta yi matukar mamaki da takaici a lokacin da ta samu labarin”.

A wata hira da aka nada, mai dauke da maganganu tsakanin dan uwan matar da kuma ministan, an tabbatar da mutumin da ya mareta minista ne saboda ta ce masa dan luwadi.

Karanta:  Albashir: ICC ta ce Afrika ta Kudu ta keta doka kan kin kama Albashir

Ya nuna cewa sauran mutanen da suke kusa da shi su ne suka kara rura wutar rikicin.

Kafofin yada labaran kasar sun bayar da rahoton cewa, rikicin ya fara ne a kan an ce waye zai gaji shugaba Jacob Zuma idan ya yi murabus, a matsayin shugaban jam’iyyar ANC a watan Disamba.

Asalin Labari:

BBC Hausa

586total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.