Mukaddashin shugaban Nigeria ya yi sabbin nade-nade

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori guda 21 a kasar.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Wnifred Oyo-Ita ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da daraktan harkokin sadarwa a ofishinta, Haruna Imrana ya fitar ranar Alhamis.

An zabo sabbin manyan sakatarorin ne daga cikin ma’aikaci 300 da suka rubuta jarrabawa don samun wannan mukami.

Sanarwar ta ce sai nan gaba, za a bayyana ma’aikatun da aka tura sabbin manyan sakatarori don fara aiki.

Ma’aikaci 300 ne daga hukumomi da sashe-sashe da kuma ma’aikatun gwamnatin tarayya suka rubuta jarrabawa don cike guraben manyan sakatarori a ma’aikatun tarayya.

Ma’aikatan sun fuskanci jarrabawa har mataki uku ciki har da batutuwan tsara manufofi da gudanar da aikin gwamnati da kuma fasahar sadarwar zamani duk a cikin mako daya.

Manyan sakatarorin sun hadar da Mu’azu Abdulkadir da Akpan Sunday da Ibrahim Wen da Adesola Olusade da Anagbobu Nkiruka.

Da kuma Ekaro Chukwumuebobo da Sulaiman Lawal da Aduda Tanimu da Folayan Olaniyi da Nabasu Bako da sauransu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

529total visits,1visits today


Karanta:  Me ya sa Osinbajo ke tsoron zakewa a mulki?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.