Mulki na dan lokaci bai dace da Afirka ba – Museveni

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya ce zama a kan kujerar mulki na dan takaitaccen lokaci ba abu ne mai kyau ba ga Afirka.

Shugaban wanda ya bayyana haka a wurin laccar farko ta tunawa da marigayi Nelson Mandela, ya ce tsohon shugaban na Afirka ta Kudu, bai iya shawo kan wasu daga cikin matsalolin da ke damun Afirka ba a lokacinsa saboda wa’adin mulki daya kawai ya yi.

A lokacin da Shugaba Yoweri Museveni ya furta wannan kalami cewa shugabanci na tsawon shekara biyar ko makamancin haka, abu ne da ba shi da kyau, masu sauraren laccar sai kawai suka fashe da dariya.

Shi dai shugaban bayan da ya jagoranci mayakansa na tawaye ne suka yi nasarar karbe mulki a shekarar 1986, ya rubuta wani littafi mai suna, ‘What is Africa’s Problem?’ (‘Mece ce matsalar Afrika?’).

A cikin littafin ne ya bayyana matsalar da yake ganin ita ce babbar abar da ke damun nahiyar ta Afirka, inda yake cewa ita ce, shugabannin da ke dadewa a kan mulki, su wuce wa’adinsu.

A yayin laccar ta tunawa da Mandela, a ranar Alhamis, sai Museveni wanda yanzu ya yi sama da shekara 30 a kan mulki ya ce shugaban Afirka ta Kudun bakar fata na farko, ya kasa shawo kan wasu matsalolin da suka addabi Afirka, kamar dunkulewar tattalin arzikinta, wanda da ya yi zai inganta rayuwar al’ummar Afirka in ji shi.

Mista Museveni ya yi shagube da cewa idan ba ka hade tattalin arzikin nahiyar ba, to wane ‘yanci kenan kake magana?

Ya ce, lokacin da Mandela ya fito daga kurkuku, na yi masa magana a kan wannan. To Mandela ba shi da isasshen lokaci saboda ya fito daga gidan sarka, kuma bai dade ba a kan mulki.

Karanta:  Gwamnatocin kasashen Arewacin Afrika na fargaban bazuwar mayakan ISIS a kasashensu

Ya kara da cewa, wasu mutane na dauka cewa zama kan mulki na dan takaitaccen lokaci abu ne mai kyau, to amma shi yana ganin hakan abu ne maras kyau, saboda ba ka da wadataccen lokaci.

Ana dai ta yada jita-jita a Ugandar kan ko shugaba Musevenin zai sauya kundin tsarin mulkin kasar domin ya samu damar sake tsayawa takara a shekara ta 2021.

A lokacin zaben dai zai haura shekara 75, ta ka’idar tsayawa zabe, to amma ya yi watsi da wannan rade-radi da cewa abu ne da ba shi da tushe.

Asalin Labari:

BBC Hausa

383total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.