Muna Nan Muna Kokari Don Ganin Buhari Ya Sake Tsayawa Zabe 2019 – El-Rufai

Wasu daga cikin ministoci da gwamnoni da wasu ‘yan siyasar kasar karkashin inuwar ‘Buharists’ na nan na kokari don ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sake tsayawa zaben shugaban kasa a shekara 2019, a cewar Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai jiya.

El-Rufai ya fadawa manema labarai a gidan gwamnati dake Abuja jim kadin kafin saduwa da tawagar Shugaba Buharin don gudanar da sallar jumma’a a babban masallacin jumma’a dake gidan shugaban kasa a Villa cewa duk wani kokari ya kamalla na ganin an sake zabar shugaban kasar, ya kara da cewa Ministan Matan Kasar da tayi ikirarin cewa Buhari yayi alkawarin mulkin zango daya kawai ne tayi furucin ne kurum a radin kanta tunda dama can bata taba marawa Buharin baya ba.

Akan maganar da ministan tayi kwanan nan, yace dama can tun da fari bata goyon bayan Buharin, amma dai tanada damar yin ra’ayin kashin kanta. Ya kara da cewa duk da cewa ta marawa Atiku Abubakar baya ne a zaben cikin gida da akayi na 2014, duk da haka Buhari ya nadata mukamin minister don tunanin cewa ta cancanta da kuma karfafawa mata guiwa a harkokin siyasa.

“Da yawa daga cikin tawagar shugaba Buhari basu goyi bayan nadata ministan ba, amma shi Buharin ya tsaya tsayin daka saboda dama can haka yake. Yana son yaga ya bawa kowa dama, ya dauki duk wani dan Nijeriya a matsayin da ko ‘ya haka ya nadata mukamin minister. Maganganun nata basu bada mamaki ba, dama can bata zama mai goyon baya ba, bata taba yarda da akidun Buhari ba. Don haka banyi mamaki ba haka kuma a matsayinta na ‘yar kasa tanada damar bayyana ra’ayinta tana kuma da damar goyon bayan duk wanda take so.

“Abin da kawai nake cewa kada ‘yan Nijeriya suyi mamaki ko su kadu. Haka dama can matsayinta yake lokaci zuwa lokaci bata goyon bayan tafiyar ‘Buharism’ ko goyon bayan abinda buhari ya tsaya a kai. Zama cikin gwamnatin Buhari wani abu ne daban, saboda gwamnati kan saka dokoki idan kana minister dole ka zartar da dokokin. Zaka iya zartar da dokokin duk kuwa da cewa kanada wata fahimtar siyasa ta daban,” a cewar ta gwamnan.

Karanta:  Buhari ya yi wa gwamnan Osun Rauf Aregbesola waya

Gwamnan ya lura cewa cigaba da zama da Alhassan a gwamnatinsa wata dama ce da shi shugaban ke da ita. Inda yake cewa “Zaka iya zama da mutum a cikin gwamnati koda kuwa baya goyon bayanka idan dai har yanada gudunmowar da zai bawa kasarsa saboda wannan gwamnatin ba  kungiyar siyasa bace mai yaki don cigaban siyasa kawai.

Mama Taraba a matsayinta na minister sau da dama tana cewa zata marawa tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar baya don zama shugaban kasa a shekarar 2019 koda kuwa Shugaba Buhari yayi nufin yin tazarce.

Gwamnan Jihar Kadunan ya musanta cewa shima yana da burin tsayawa takarar shugaba kasa, inda yake cewa “Abin kawai da nake son fadi a bayyane anan shi ne ban taba zama dan takarar shugaban kasa ba. Kai ban taba koda zama dan takarar gwamna ba. Anata yayata sunana tun shekarar 2007 a matsayin dan takarar shugaban kasa bayan shekarun da na shafe a matsayin minister a birnin tarayyar kasar.

Babu wani abu sabo a game da haka. Abin da nake son fada a bayyane kawai anan shi ne ban taba zama dan takarar shugaban kasa ba, kai ban taba zama dan takarar gwamna ba. Ina matsayin gwamna a yau saboda Allah Ya yarda saboda kiran da Buhari ya yi min cewa inje inyi takarar gwamna a jihar Kaduna. Amma matsayina game da abinda ya shafi zaben 2019 shi ne shugaba na cikin yanayi mai kyau yana kuma murmurewa sosai. Fatana da addu’a ta shi ne ya sake tsayawa a shekarar 2019.”

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

1251total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.