Musulmi a Kano sun gudanar da taron addu’o’i don Shugaba Buhari

Dubun dubatar Musulmi daga jihohi bakwai na Arewa Maso Yamma sunyi taron gangami a Kano yau din nan don gudanar da addu’o’i na musamman ga  shugaba Muhammadu Buhari.

Jihohin sun hada da Kano, Jigawa, Katsina, Sokoto, Kebbi, Zamfara da Kaduna.

Taron addu’o’in wanda yanzu haka ake gudanar da shi a Rufaffan Dakin Taro na Sitadiyon din Sani Abacha ya hada manya Malamai, ‘Yan siyasa, Manyan Jami’an Gwamnati da Daruruwan Mambobin Kungiyoyin Fararen Hula, Kungiyoyin Dalibai da Sauran Kungiyoyin da ba na gwamnati ba.

Ana sa ran taron zai gudanar da sallah raka’a biyu da addu’o’i sannan ayi maci zuwa gidan gwamnatin jihar inda aka shirya Gwamna Ganduje zai gana da mahalarta taron.

Maibawa Shugaba Muhammadu Buhari Shawara ta Fuska Rediyo da Talabijin, Alhaji Ibrahim Sha’aban Sharada ne ya shirya taron inda yake cewa an shirya taron ne don yiwa Allah godiya da ya kare lafiyar shugaban kasar.

A cewarsa “Mun shirya wannan taron ne don yiwa Allah godiya da ya kare lafiyar masoyinmu Shugaban Kasa wanda ya samu komowa daga hotun rashin lafiya kwanan nan. Shugaban ya warke kwarai da gaske ya kuma dawo gida Nijeriya lafiya.”

889total visits,1visits today


Karanta:  Ba zan nemi gafarar Buhari ba – Buba Galadima

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.