Mutane 40 Sun Mutu a Zabtarewar Kasa a Congo

A kalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu sakamakon zabtarewar kasa da ta lullube wani dan karamin kauyen masunta a Jamhuriyar Demokradiyar Congo a gabar kogin Albert da ke yankin Ituri a arewa maso gabashin kasar.

Pacifique Keta mataimakin gwamnan yankin Ituri ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labara na AFP cewa lamarin ya faru ne a kauyen Tora, in da mutane 40 suka rasa rayukansu.

Shugaban asibitin Tshomia da ke Tora a yankin Ituri,  Hervé Isamba ya ce, mutane 4 sun tsira da rayukansu daga cikin wadanda aka kwantar su a asibitin don karbar magani.

Su dai masuntan da ke gabar kogin Albert sun dauki sana’ar  su da mahimmanci, in da ta fi samar wa mafi yawan mutan yankin na Ituri mai arzikin Zinare da ke kan iyakar kasar ta Congo da Ouganda kudaden shiga.

A baya dai Jamhuriyar Demokradiyar Congo, ta sha fama da matsalar zaftarewar kasa da ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, a 2010 malalar tabon laka ta ratsa kauyen Kibiriga da ke gabashin kasar, in da mutane 19 suka rasa rayukansu a yayin da wasu 27 suka bata.

Sai kuma a watan Fabairun 2002, in da sama da mutane 50 suka rasa rayukansu sakamakon zaftarewar kasar da ta biyo bayan ruwan sama mai yawan gaske da aka samu a garin Uvira da ke gabashin kasar, in da sama da mutane 2,500 suka rasa mahallansu.

Wannan bala’in zaftarewar kasar dai ya zo ne bayan da aka samu ambaliyar ruwa da zabtarewar laka a Freetown na Saliyo, in da mutane sama da 300 suka mutu, yayin da kimanin 600 suka bace.

Asalin Labari:

RFI Hausa

936total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.