Mutane 600 sun bace a ambaliyar Saliyo

Akalla mutane 600 sun bace bayan zabtarewar laka da ambaliyar ruwa da suka afka wa wasu yankuna na babbab birnin Freetown da ke Saliyo.

An dai tabbatar da mutuwar mutane kusan 400 bayan aukuwar ibtila’in a farkon wannan makon.

A yau Laraban ne ake saran gudanar da jana’izar wasu mutanen da suka rasa rayukansu, matakin da zai rage cinkoson gawarwakin da aka jibge a dakunan ajiye gawarwaki.

Tuni shugaban kasar Ernest Bai Koroma ya bukaci taimakon gaggawa daga kasashen duniya, in da ya ce, ambaliyar ta share wuraren zaman al’umma.

Shugaban ya kuma bukaci jama’a da su kaurace wa yankunan da ibtila’in ya auku.

Asalin Labari:

RFI Hausa

443total visits,1visits today


Karanta:  Amurka Tana Tunanin Ko Ta Dauki Matakin Soja Kan Venezuela

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.