Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Gwabza Fada Tsakanin ‘Yan Kwankwasiyya Da ‘Yan Gandujiyya A Kano

Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dr. Rabi’u Suleiman Bichi da kanin tsohon gwamnan jihar Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso na daga cikin mutane da daman da suka ji rauni jiya sakamakon gwabza fada tsakanin magoya bayan darikar Kwankwasiyya da Gandujiyya.

Sauran wadanda aka jiwa rauni a fadar mai martaba lokacin da ake gudanar da Hawan Dushen jiya sun hada da Dr. Adamu Yunusa Dangwani, Komared Aminu Abdussalam wadanda dukkaninsu tsofaffin Kwamishinoni ne karkashen gwamnatin Kwankwason da ta gabata.

Da yake tabbatar da lamarin ga majiyar Daily Trust ranar lahdi, Dr Dangwani cewa yayi “Muna tsaka da kallon mahaya dawaki kwatsam sai magoya bayan Gandujiyya suka far mana. Suka doki tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha da wani katon sanda suka kuma dabawa Yahya wuka a kafada.”

Ya kuma ce sannan suka raunata ‘yan Kwankwasiyya da dama kafin ‘Yan sanda su kawo dauki inda suka tsairar da sauran ‘yan Kwankwasiyar.

Ya kara da cewa “An garzaya da Tsohon Sakataren Gwamnatin da Dan Uwan Kwankwaso zuwa Asibitin Malam Aminu Kano domin duba lafiyar su inda daga baya aka sallamesu.”

Yace har yanzu suna tattara bayanan adadin wadanda aka jiwa raunin za kuma su gana da ‘Yan Jirida nan gaba kadan a yau dinnan.

Tuni Dan Majalisar Jiha mai wakiltar Cikin Birnin Kano wanda ake zargi da bada umarnin kaiwa ‘Yan kwankwasiyyar farmakin yayi watsi da zargin da akeyi masa.

A cewar Dan Agundi “Zargin ba gaskiya bane. Yaya za ace mai yin doka ya dau doka a hannunsa? Wannan abu ne da ba zai taba yiyuwa ba. ‘Yan Kwankwasiyya kamata yayi su tabbatar da hakan yadda kowa zai gamsu.

Karanta:  Bamusan Inda Ganduje Ya Dosa Ba – Danburam Nuhu Yakasai

“Yanzu muna cikin zamani Fasahar Sadarwa sai su tabbatar da zargin ta hanyar kwararan hujjoji. Mu dai muna da hotunan bidiyon abubuwan da suka faru a hawan dabar.”

Inda yake tofa albarkacin bakinsa Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Malam Muhammad Garba cewa yayi “A iya sanina babu wani yamutsin da ya faru a Hawan na Daba. Ban gani da idanuna ba don haka bazan tabbatar da lamarin ba.

“Idan har akwai wani yamutsi a wani gurin to ni ban sani ba. Amma ni abin da zan iya tabbatar muku na gasgiya shi ne banga komai ba.”

Asalin Labari:

Daily Trust, Muryar Arewa

1655total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.