Mutane Milliyan 9 a Afrika Na Iya Mutuwa Saboda Katse Tallafin HIV

Sakamakon wani bincike ya nuna cewa akalla mutane miliyan 9 zasu rasa rayukansu a kasashen Afirka ta kudu da Cote D’Ivoire sakamakon katse tallafin kudaden taimakawa masu fama da cutar kanjamau da shugaban Amurka Donald Trump yayi.

Wani binciken farko da aka gudanar kan illar janye tallafin da Amurka tayi, ya nunawa masana kimiya cewar matsalar za tafi kamari a kasashen Afirka.

Rahotan yace kashi 19, na manyan mutane a Afirka ta Kudu na dauke da cutar mai karya garkuwar jiki, kuma suna bukatar agajin, sai kuma Cote d’Ivoire mai mutane dubu 460,000.

Masana kimiyar daga kasashen Amurka, Afirka da kuma Turai sun ce muddin ba’a samu sauyi ba, akalla mutane kusan miliyan 2 zasu mutu nan da shekaru 10 masu zuwa.

Asalin Labari:

RFI Hausa

406total visits,2visits today

Karanta:  'An yaudari manyan jami’an Donald Trump'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.