Mutum nawa ne suka gana da Buhari a London?

Jami'an gwamnatin Najeriya daban-daban sun gana da Shugaban Kasar Muhammadu Buhari a birnin Landan na kasar Birtaniya, inda ya kwashe fiye da wata uku yana jinya.

Rashin lafiyar Shugaba Buhari, wanda ya fice daga kasar ranar 8 ga watan Mayu a karo na biyu a shekarar 2017, ta ja hankalin ‘yan kasar da ma wasu kasashen duniya.

Wasu dai na yin kira ga shugaban ya sauka daga mulki saboda rashin koshin lafiyarsa.

Sun kara da bayar da hujja cewa shi kansa shugaban na cikin mutanen da suka rika kiraye-kirayen marigayi Shugaban Kasar Umaru Musa ‘Yar Adua ya sauka daga mulki lokacin da ya kwanta jinya.

Sai dai jami’an gwamnatinsa sun sha nanata cewa babu wata hujja da za ta sa Shugaba Buhari ya ajiye mukaminsa saboda, sabanin marigayi ‘Yar Adua wanda bai mika mulki ga mataimakinsa kafin ya kwanta rashin lafiya ba,

Shugaba Buhari ya mika mulki ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, inda yake tafiyar da kasar a matsayin mukaddashin shugaban kasa.

Da alama kiraye-kirayen da ake yi ga shugaban ya sauka daga mulki da kuma wasu rahotanni da suka rika yawo cewa yana halin rai-kwa-kwai-mutu-kwakwai ne suka sa jami’an gwamnati da gwamnoni da ‘yan siyasa suka rika kai masa ziyara a baya bayan nan domin su nuna ainihin halin da yake ciki.

Su waye suka kai masa ziyara?

Baya ga mai dakinsa Aisha Buhari, wadda sau da dama tun lokacin da ya koma Landan domin a duba lafiyarsa, Mukaddashin Shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya kai masa ziyara ranar 11 ga watan Yuni, kuma bayan komawarsa gida ya shaida wa manema labarai cewa “mun tattauna da kyau da shi [Shugaba Buhari] kan abubuwa da dama kuma yana cike da annashuwa. Yana samun sauki sosai.”

A cewarsa ko da yake shugaban bai gaya masa lokacin da zai koma gida, amma “Ina ganin a nan gaba kadan zai koma. Nan ba da jimawa ba. Ina ganin ya kamata mu tsammanci dawowarsa. Kamar yadda na fada yana samun sauki sosai.”

Karanta:  Buhari Ya Bada Damar Gina Layin-Dogo Daga Kano Zuwa Daura Kasarsa Ta Haihuwa

Farfesa Osinbajo bai ko gama hutawa daga ziyarar da ya kai wa mai gidan nasa ba ne sai ayarin gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki da shugaban jam’iyyar suka kai masa ziyara ranar 23 ga watan na Yuni.

Tawagar da ta kai masa ziyara ta kunshi gwamnonin jihohin Kaduna da Nasarawa da Imo da Ministan Sufuri Mista Rotimi Amaechi da kuma Shugaban Jam’iyyar APC John Oyegun.

Bayan ganawar, shugaban gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Imo Cif Rochas Okorocha ya shaida wa BBC cewa sun yi mamakin yadda suka ga irin saukin da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu.

Gwamnan ya kara da cewa shugaban yana cikin koshin lafiya “kuma zancen da ake yi cewa yana cikin mawuyacin halin ba gaskiya ba ne. Yana nan lafiya lau. Muna ganin daga nan zuwa sati biyu insha Allah zai koma gida ya ci gaba da aikinsa.”

Ya kara da cewa “Shugaba Buhari ya gaya mana cewa da zarar likita ya sallame shi zai komo gida. Kuma da ni ne likitan zan sallame shi ganin yadda jikinsa ya yi kwari”.

Kazaliza ranar 26 ga watan Yuni gwamnoni bakwai, ciki har da na jam’iyyar PDP mai hamayya, sun kai wa Shugaba Buhari ziyara.

Gwamnonin sun hada da Abdulaziz Yari na jihar Zamfara, da Dave Umahi na jihar Ebonyi, da Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, da Kashim Shatima na jihar Borno, da Samuel Ortom na jihar Benue, da kuma Abiola Ajumobi na jihar Oyo.

Sai kuma ranar hudu ga watan Agusta, inda Shugaban Cocin Ingila, Archbishop na Canterbury, Justin Welby, ya ziyarci ga Shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari a gidan da ake kira Abuja House da ke London.

Karanta:  Aisha ta gargadi Muhammadu Buhari

Welby ya ce ya ji dadin ganin Buhari

“Na yi farin ciki kan yadda na ga Buhari ya murmure cikin sauri,” in ji jagoran cocin.

A baya ma dai jagoran cocin ya kai ziyara ga shugaban, lokacin da ya yi jinya a farkon shekarar nan.

Ganawa ta karshe da shugaban na Najeriya ya yi ita ce ziyarar da ministan watsa labarai Alhaji Lai Mohammed ya jagoranci wasu jami’an watsa labaran shugaban kasar ranar 12 ga watan Agusta.

Cikin wadanda ya gana da su har da babban mai taimaka masa kan watsa labarai da hulda da jama’a, Mallam Garba Shehu da mai ba shi shawara kan watsa labarai Femi Adesina da mai daukar hotonsa Bayo Omoboriowo.

Hotunan da aka dauke su tare da shugaban, sun nuna shi cikin raha kuma yana tafiya, ba kamar na baya ba inda akasari yake a zaune.

Shugaba Buhari ya shaida wa bakin nasa cewa ya samu sauki sosai amma dole ya jira umarnin likitocinsa kafin ya koma gida.

Sai dai akwai mutanen da wasu ‘yan kasar ke gani ya kamata su gana da shugaban na Najeriya amma har yanzu bai gana da su ba.

Mutanen kuwa su ne shugabannin majalisun tarayya — majalisar dattawa da ta wakilai — Bukola Saraki da Yakubu Dogara.

A lokacin da ya yi jinya a baya dai, suna cikin mutanen da suka kai masa ziyara sai dai rashin kai ziyararsu a wannan karon ya sa ‘yan kasar na ganin da walaki, goro a miya.

Kazalika shugaban ya yi ganawa da rukunin mutane na karshe ne a daidai lokacin da wasu ‘yan kasar suka yi zanga-zangar kira a gare shi ya koma kasar ko kuma ya sauka daga mulki a Abuja, babban birnin kasar.

Karanta:  Buhari ya gana da wasu gwamnoni a London

Sai dai su ma wasu magoya bayan shugaban sun yi nasu gangamin inda suka yi kira a gare shi ya ci gaba da hutawa har sai ya samu sauki sosai yadda zai iya ci gaba da aiki.

Aisha Buhari ta ce mai gidanta zai koma Najeriya ya yi maganin kuraye.

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

 • 19 ga watan Jan – Ya tafi Birtaniya domin “hutun jinya”
 • 5 ga watan Fabrairu – ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
 • 10 ga watan Maris – Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
 • 26 ga watan Afrilu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma “yana aiki daga gida”
 • 28 ga watan Afrilu – Bai halarci Sallar Juma’a ba
 • 3 ga watan Mayu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
 • 5 ga watan Mayu – Ya halarci sallar Juma’a a karon farko cikin mako biyu
 • 7 ga watan Mayu – Ya koma Birtaniya domin jinya
 • 25 ga watan Yuni – Ya aikowa ‘yan Najeriya sakon murya
 • 11 ga watan Yuli – Osinbajo ya gana da shi a London
 • 23 ga watan Yuni – Ya gana da wasu gwamnonin APC da shugaban jam’iyyar

 

1477total visits,7visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.