Nafisa Abdullahi Ta Zama Jakadiyar LEADERSHIP A YAU

An kammala shirye-shirye tsakanin kamfanin buga jaridun LEADERSHIP da fitacciyar ’yar wasan Hausa, wacce kuma ta yi suna wajen fita a matsayin mai hakuri a finafinanta, wato Nafisa Abdullahi, inda ta zama Jakadiyar LEADERSHIP A YAU.

Bayan kulla wannan yarjejeniya, Nafisa Abdullahi ta bayana cewa, “da farko dai ina mika godiya ta ga Kamfanin Rukunan Jaridun LEADERSHIP. Na yi mutukar farin cikin kasancewa ni ce Jakadiyar LEADERSHIP A Yau ta farko. Yadda aka dauke ni da muhimmanci ne ya sa har ake so a mayar da ni Jakadiya Jaridar LEADERSHIP A Yau. Duk a tarin Jaruman da suke Nijeriya, an dauke ni, ni ce ta farko wanda aka ba ta wannan babban matsayi. Don haka ina mutukar farin ciki.”

Ta ci gaba da bayyana cewa, “lalle zan bada karfin gwiwa don in ga wannan alakar tamu ta dore fiye da yadda muke tunanin za mu samu .”

Jaruma Nafisa Abdullahi ba ta kammala jawabinta ba sai da ta yi kira ga al’umma, ta ce, “ina kira ga jama’ar gida Nijeriya  dama kasashen waje, su rinka karanta jaridar LEADERSHIP A YAU, domin za su rinka ganin abubuwa daban-daban wadanda za su ilimantar, fadakarwa da kuma nishadantar da su.

Da yake nuna jin dadinsa da wannan hulda, Mukaddashin Manajan Daraktan sashen LEADSRSHIP A YAU, Stanley Kingsley Nkwocha ya nuna matukar jin dadinsa da wannan dangantaka da Jarumar, inda ya yi fatan cewa wannan huldar jakadanci za ta zamam hanyar da za a amfani juna tsakanin Jarumar da kuma LEADERSHIP A YAU.

Asalin Labari:

LEADERSHIP AYAU

3138total visits,1visits today


One Response to "Nafisa Abdullahi Ta Zama Jakadiyar LEADERSHIP A YAU"

  1. Umar sani   September 14, 2017 at 12:38 pm

    Allah ya taimaka

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.