Najeriya: MDD Ta Dakatar Da Shirin Raba Abinci a Sansanin Gubio

Bayanai masu karo da juna sun nuna cewa hukumar samar da abinci ta WFP ta dakatar da ayyukan raba abinci a wani sansani da ke jihar Bornon Najeriya bayan da aka zargi 'yan gudun hijrar da kai wa ma’aikatanta hari saboda ana yawan basu tuwo babu sirki.

Hukumar da ke kula da shirin samar da abinci ta WFP dake karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ta dakatar da ayyukan samar da abinci ga ‘yan gudun hijra da ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijra da ke Gubio a jihar Borno.

Hukumar ta dauki wannan mataki ne saboda far ma ma’aikatanta da ‘yan gudun hijrar suka yi a sansanin na Gubio mai dauke da dubban ‘yan gudun hijra.

Wasu bayanai sun nuna cewa ‘yan gudun hijrar sun kai wa ma’aikatan hukumar hari ne saboda sun gaji da abincin tuwo da ake ba su babu kakkautawa ba tare da samun sirkin wani abinci ba.

Amma shugaban ba da agajin gaggawa na jihar Borno Engineer Ahmed Satomi ya ce bayanan da jami’ansu suka tattaro daga sansanin na Gubio sun nuna cewa ba saboda yawan ba da tuwo ba ne ya haifar da rikicin.

“Abinda ya faru Gaskiya an dauki wasu lokuta kamar kusan mako guda da ba a kawo abincin akan lokaci ba, mun kuma yi magana da ‘yan WFP akan cewa suna da matsala da hanyoyin masu samar da abinci.”

A karshen makon da ya gabata ne wasu ‘yan gudun hijra suka kai hari akan ma’aikatan hukumar ta WFP inda har suka farfasa motocin da suke ciki.

To shin ko an dakatar da ba da abincin a sansanin ‘yan gudun hijrar na Gubio ke nan?

Asalin Labari:

VOA Hausa

674total visits,4visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.