Najeriya Ta Lashe Gasar Kwallon Kwando Ta Nahiyar Africa

Tawagar 'yan wasan kwallon kwando ta Najeriya D'Tigress da ta lashe kofin gasar ta nahiyar Afrika a Bamako, Mali.

Tawagar kwallon Kwando ajin mata da ke wakiltar Najeriya, wato D’Tigress, ta samu nasarar lashe kofin gasar kwallon Kwando ta nahiyar Africa, karo na uku, da ta gudana a babban birnin Mali, Bamako.

Najeriya ta samu nasarar ce bayan lallasa kasar Senegal da kwallaye 65 da kuma 48 a wasan karshen da suka fafata a jiya Lahadi.

Ko wasan rukuninsu na B da suka fafata a farkon wannan gasa, ‘yan matan kwallon kwandon na Najeriya, sun lallasa tawagar Senegal da kwallaye 58 da kuma 54.

Ba dai a wannan karon bane kadai Najeriya ke doke Senegal a wasan karshen na cin kofin kwallon kwandon nahiyar Afrika ajin mata, domin a shekara ta 2005 D’ Tigress din sun lallasa Lionesses din na Senegal da kwallaye 64 da kuma 57 a garin Abuja.

Yanzu haka dai Najeriya na da kofunan wannan gasa har uku, shekara ta 2003, 2005, da kuma wannan ta 2017.

Asalin Labari:

RFI Hausa

670total visits,1visits today


Karanta:  Messi Yana Jan Kafa Wajen Sabunta Yarjejeniya Da Barcelona

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.