Najeriya Ta Yi Maraba Da Batun Sayen Jiragen Yaki Daga Amurka

Najeriya ta yi maraba da kudurin gwamnatin Amurka na amincewa sayar mata da jiragen yaki, al’amarin da a baya ya janyo cece-kuce tsakanin kasashen biyu.

Gwamnatin shugaba Donald Trump za ta sayarwa da Najeriya jiragen yaki na zamani da ake kira A-29 Super Tucano har guda 12.

Gwamnatin Najeriya ta yi maraba da wannan mataki, kamar yadda babban jami’i a ofishin mukaddashin shugaban Najeriya Alhaji Hafizu Ibrahim ke cewa gwamnatin Amurka ta gamsu da shugabancin Buhari da mataimakina.

A baya dai Amurka ta tayi ta saka tarnaki wajen sayarwa da Najeriya makamai, bisa zargin dakatun kasar na danne hakkin bil Adama a dai-dai lokacin da mayakan Boko Haram ke rawar gaban hantsi.

A cewar kwararre a fannin jiragen yaki, jirgin yakin A-29 Super Tucano jirgi ne da komi dare zai iya tashi ba tare da yayi wani kara ba, yana kuma iya ganowa da kuma kaiwa ‘yan ta’adda hari ba tare da sun iya kakkabo shi ba.

Amurka tayi amfani da ire-iren wannan jirage a yakin da tayi da ‘yan kungiyar Taliban a Afghanistan.

Shi kuma masanin tsaro a Najeriya, Al-mustapha Liman, na ganin sojojin Najeriya kadai sun isa kawo karshen Boko Haram ba tare da an sayo sabbin jiragen yaki ba, inda ya ce zance ne na zama domin samo bakin zaren warware matsalar.

Asalin Labari:

VOA Hausa

554total visits,1visits today


Karanta:  Kotun Turai ta yi watsi da bukatar Hungary da Slovakia kan 'yan gudun hijira

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.