NAPTIP ta fitar da runduna ta musamman domin yaki da fataucin mutane

Babban darakta ta Hukumar yak da fataucin mutane (NAPTIP), Ms Julie Okah-Donli, ta kaddamar da runduna ta musamman da za ta taimaka wajen yaki da fataucin mutane.

Jami’i mai kula da huldar jama’a da ‘yan jaridu, Mr Josiah Emerole ne ya sanar da hakan ga ‘yan jaridu, yau Talata a Abuja. Ya kara da cewar wannan ci gaban ya biyo bayan kokarin sabon shugabancin wajen gyarawa hukumar zama don gudanar da aiki ga jama’a.

Emerole ya ce wannan runduna za ta yi aiki kai tsaye bisa kulawar Babbar darakta. Dadin dadawa kuma, za a tabbatar da cewar dukkanin manyan korafe -korafe da aka gabatar a gaban hukumar, an yi bincike akai da ba su kulawar da ta dace.

 

Asalin Labari:

NAN,TODAY NG, MURYAR AREWA

625total visits,1visits today


Karanta:  Matasan Katsina sun nesanta kansu da kalaman Sarkin Katsina kan Inyamurai

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.