Navas zai yi wa Sevilla wasa kan yarjejeniyar shekara hudu

Dan wasan tawagar Spaniya, Jesus Navas, ya sake komawa Sevilla bayan da Manchester City ta sake shi.

Navas, mai shekara 31, ya koma City ne daga kungiyar kwallon kafar da ke buga wasa a gasar La Liga kan yarjejeniyar shekara hudu da ta kai Fam miliyan 14.9 a watan Yunin shekarar 2013.

Ya buga wa City wasa 173 inda ya ci kwallo takwas, amman wasanni 124 kawai ya buga a kakar bara.

Kwantiragin Navas da City ya kare a lokacin bazara, lamarin da ya sa ya koma Sevilla, inda zai murza-leda, kan yarjejeniyar shekara hudu.

Yana cikin tawagar Sevilla da ta ci kofin Uefa a shekarar 2006 da 2007, amman ya yi tsananin kewar gida da yawa, lamarin da ya sa ya ki amincewa da tayin da aka masa na zuwa Chelsea a shekarar 2006.

Navas zai kafa tarihi a matsayin wanda ya fi taka wa Sevilla leda in ya kara buga wa kulob din wasa 27. Ya buga wasa 393 a zamanshi na farko a kungiyar yayin da Juan Arza Inigo ya kafa tarihin buga wa kungiyar wasanni 419.

Asalin Labari:

BBC Hausa

2658total visits,2visits today


Karanta:  Neymar ya Caccaki Daraktocin Barcelona

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.