Neman Gurbin Zuwa Gasar Kwallon Kafa Ta Duniya: Nijeria Ta Casa Kamaru

‘Yan Wasa Kwallon Kafar Nijeria da ake kira Super Eagles sun casa ‘Yan Wasan Kwallon Kafar Kasar Kamaru da ake yiwa take da Indomitable Lions 4:0 a wasan da suka buga a Sitadiyon din Godswill Akpabio dake garin Uyo na Akwa Ibom ranar Jumma’a don neman gurbin shiga gasar kwallon kafa ta duniya.

Wadanda suka ci kwallayen sun hada da dan wasan gaba Odion Ighalo, da Kaftin din kungiyar, Mikel Obi, sai dan wasan gefe na kulub din Chelsea Victor Moses, sai kuma dan wasan nan da tauraronsa ke haskakawa na kulub din Leicester City wato Kelechi Iheanacho.

A dai dai minti na 29 ne Odion Ighalo ya saka kungiyar kwallon kafar Nijeria gaba sakamakon jefa kwallo a raga da yayi ta hanyar kwallon da Obi Mikel ya mika masa.

Shi kuwa John Mikel Obi ya kara kwallo ta biyu a raga a dai dai minti na 42.

Moses Simon shi ya taimaka aka ci kwallo ta ukun da Victor Moses yayi a dai dai minti na 55.

Shi kuwa Kelechi Iheanacho yaci kwallo mai ban kaye da ka a dai dai minti na 76.

Nijeriya ke jagorancin rukunin da maki 9, sai kuma Kamaru ta biyu da maki biyu, sai kasar Zambia da kasar Algeria dake da maki guda guda kowannensu.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

331total visits,1visits today


Karanta:  Man City ta sayi Walker kan fam 45m

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.