Neman ‘yan Boko Haram ne ya kai mu ofishin MDD – Sojin Nigeria

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun gudanar da bincike kan gida 30 ciki har da wani ginin Majalisar Dinkin Duniya don neman wasu manyan 'yan Boko Haram a Maiduguri.

Ta ce binciken ya biyo bayan wasu sahihan bayanai da ta samu cewa wasu manyan ‘yan Boko Haram sun yi satar shiga yankin Pompomari Bye Pass.

Sanarwar wadda rundunar ta fitar ranar Juma’a a Maiduguri ta ce a tsawon mako guda da ta yi tana aikin killacewa da bincike, ta bankade unguwannin a Jiddari – Polo da Garejin Muna da Jakana da sauran wurare.

Ta ce aikin wani kandagarki ne ta hanyar gudanar da bincike a kan ko ina da ina ciki har da wannan gini wanda ta ce babu wata alama da ta nuna ginin Majalisar Dinkin Duniya ne.

Sanarwar ta ce duka-duka aikin da ta yi a daukacin yankin ya yi nasara, ko da yake ba ta kama kowa ba saboda ba ta gano wani da ake zargi ba.

Kafofin sada zumunta a cikin jihar Borno sun yi ta yada bayanan cewa, sojoji sun gudanar da binciken ne a ginin, a kokarinsu na gano shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.

A ranar Juma’a ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dakarun tsaron Nijeriya sun kai samame kan daya daga cikin ofisoshinta a yankin arewa maso gabashin kasar, inda suka gudanar da bincike ba tare da izini ba.

Wata mai magana da yawun Majalisar ta fada wa BBC cewa an kaddamar da binciken ne, na tsawon sa’a uku da sanyin safiyar Juma’a a birnin Maiduguri.

Majalisar Ɗinkin Duniya na da yawan jami’ai a arewa maso gabashin Najeriya, inda suke bayar da tallafi ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.

Ta bukaci ma’aikatanta ‘yan asalin yankin su yi aikinsu daga gida a ranar Juma’a sakamakon faruwar lamarin.

Karanta:  Zan Yaki 'Yan Ta'adda da Miyagu – Buhari

Ta kuma ce ta sauke jiragen helikwaftanta da ke samar da ayyukan agaji ga sansanonin da ke da nisa a matsayin wani mataki na riga-kafi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

581total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.