Neymar zai yi wa PSG wasa a yau Lahadi

Dan kwallon tawagar Brazil, Neymar zai buga wa Paris St-Germain wasan farko a gasar Faransa a yau Lahadi.

Hukumar da ke gudanar da gasar Faransa ce ta samu tabbacin kammala cinikin Neymar kan fam miliyan 200 daga Barcelona.

Saboda haka dan kwallon mai shekara 25, zai yi wa PSG wasansa na farko a karawar da za ta ziyarci Guingamp a ranar ta Lahadi a makon farko a Ligue 1.

Kocin PSG, Unai Emery ne ya tabbatar da cewar Neymar yana cikin koshin lafiya ya kuma shirya buga wa kungiyar tamaula.

Neymar ya koma PSG daga Barcelona a makon jiya, sai dai ya gamu da tsaiko, bayan da hukumar kwallon Spaniya ba ta bayar da takardun amincewa ya koma Faransa da taka-leda da wuri ba.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1686total visits,4visits today


Karanta:  Man City za ta Kafa Tarihi Wajen Sayan Messi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.