Ni Nake Bin Barcelona Kudi — Neymar

Dan kwallon Paris St-Germain, Neymar zai kalubalanci Barcelona kan kararsa da ta shigar a Spaniya.

Barcelona na son dan kwallon ya biya fam miliyan 7.8 ladan wasa da aka ba shi a lokacin da ya tsawaita yarjejeniyar zama a kungiyar zuwa shekara biyar, wata tara kafin ya koma Faransa.

Dan wasan na Brazil ya koma PSG a cikin watan Agusta kan fam miliyan 200, bayan da ya biya kunshin yarjejeniyar da Barcelona ta ce sai an biya idan kwantiraginsa bai kare ba.

Lauyan Neymar zai kalubalanci Barcelona kuma ya fitar da zawabin dan kwallon mai shekara 25.

Neymar ya ce shi ne yake bin Barcelona kudi bisa barin Nou Camb, ba wai ita ce ke neman hakki a wajensa ba.

A jawabin da suka fitar ”Kan ladan wasan da Neymar ke bin Barcelona a yarjejeniyar 2016, yana da muhimmaci na sanar da cewar dan wasan ya fara shirin yadda zai karbi hakkinsa a kotunan da suka da ce”.

A ranar Talata Barcelona ta bukaci Neymar ya dawo da ladan wasa da ”tuni ta biya shi” da karin kaso 10 cikin dari kan lattin kin biyan kudin.

”Kungiyar tana neman ya biyata kudin ne, saboda bai karasa yarjejeniyar da ya kulla da ita ba” kamar yadda ta ce.

Asalin Labari:

BBC Hausa

864total visits,2visits today


Karanta:  Inter Milan za ta iya sayar da Ivan Perisic ga Man United

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.