Ni Yakamata Ku Farwa, Ba ‘Yan Kabilar Igbo Ba, Sako Daga Sarkin Musulmi Zuwa Samarin Arewa

Daga Sokoto- Maigirma Sarkin Musulmi Sultan Abubakar ya ce duk wanda yake da shirin kaiwa ‘yan kabilar Igbo mazauna arewacin kasar hari, to shi yakamata ya fara kaiwa wannan harin.

Sarkin musulmin ya fadi haka ne lokacin da shugaban kabilar Igbon ta duniya, Dr Mishack Nnanta tare da rakiyar shugabannin kabilar Igbo mazuna yankin suka kai masa ziyarar barka da sallah a fadarsa.

“Idan har wani mutum ko taron mutane suka shirya wani abun da bai dace ba akan ‘yan kabilar Igbo, duk wanda ko wadanda sukayi nufin hakan to kamata yayi su fara ta kaina saboda nayi hannun riga da ummarnin da matasan arewa suka baiwa ‘yan kabilar Igbo na ficewa daga yankin,” a cewarsa.

Sarkin na musulmi Abubakar ya lura cewa “samar da gyare-gyare a kasa” baya nufin gallazawa ko raba kasa Nijeriya, abin da kawai yake nufi a fahimtarsa shi ne a samar da sauye-sauye nan da can don samar da adalci ga kowa a kasa bakidaya a addinance da yanayin zamantakewa dama tattalin arziki.”

Ya kuma a lura da cewa yikurin da wasu mutane keyi na neman a raba kasar “ba zai magance matsalolin da suke addabar kasar ba haka kuma raba kasar zuwa yanki-yanki ba shi ne mafita ga daukacin matsalolin da suke damfare a kasar ba abin da zai haifar kawai shi ne neman ‘yancin kai ga garuruwa da kyauyika.“

A ganinsa mafita kawai ita ce a zauna a teburin shawara  da fahimtar juna ba wai daukan makami ba wanda ba zai haifar da zaman lafiya ba. Ya yarda da cewa akwai korafai-korafan da suke nuna cewa ana danne wadansu, Sarkin yace mafita kawai ita ce kawo sauyi cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Karanta:  'Yan Biafra 'yan ta'adda ne — Sojin Nigeria

Ya zargi ‘yan siyasar kasar kan mafi yawan matsalolin dake addabar ‘yan kasar inda yake cewa

“Zasu zo muku a lokacin kamfen da dadin baki da alkawarurrukan da bana gaskiya ba kamar  samar da na’urar sanyaya daki a akan titunanku da baku madara a bakunanku kowanne lokaci ba tare da kunyi wani namijin kokari ba. Daga sunci zabe sun tafi Abuja zasu fara shiryawa kansu ingantacciyar rayuwa ne kawai wadanda suke a kyauyuka su koma birane da zama, suyi watsi da wadanda suka dangwala musu kuri’a.” a cewarsa

Tun da fari Nnanta cewa yayi ‘yan kabilar ta Igbo mutane ne masu son zama lafiya wadanda abun da suka saka a gaba shi ne harkokin kasuwancin su.

“Igbo ba zasu iya zama lafiya ba idan har suka ware daga Nijeriya. Don haka kamata yayi su taimaka wajen kasancewar Najeriya kasa guda ta hanyar samar da canjin da ya dace kamar yadda Janar Yakubu Gawon yayi alkawari. Zasu iya kira da a kara musu jihohi a yankin su na Kudu maso Gabas don suma su hada kafada da sauran yankunan kasar,” a cewarsa.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

516total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.