Niger: ‘Da Gangan Aka Kashe Dalibin Jami’a’ Mala Bagale’

Kwamitin da gwamnatin Jamhuriyar Niger ta kafa domin binciken sanadin mutuwar wani dalibin jami'a yayin wata tarzoma da jami'an tsaro ya fitar da rahotonsa.

A watan Afrilu ne marigayi Mala Bagale dalibin jami’ar Abdou Moumini Dioffo da ke birnin Niamey ya mutu yayin wata zanga-zanga; a cikin wani yanayi da ya jawo takaddama kan abin ya yi sanadin mutuwarsa.

Takwarorinsa dalibai dai sun ce sojoji ne suka harbe shi, yayin da jami’an gwamnati suka ce ya rasu ne sakamakon faduwar da ya yi kan wani dutse.

Sai dai da yake sanar da sakamakon binciken, kwamitin ya ce dalibin ya mutu ne bayan da wani abu ya buge shi a kai; ba ya mutu ne don ya fadi da kansa bisa wani dutse ba kamar yadda aka fada.

”Binciken da muka yi mu a kwamiti, na farko mun nemi likitoci masu sa gawa ta yi magana sai wannan malamin (likitan) ya ce ai wannan dalibin makaranta abin da ya kashe shi wani abu ne ya zo ya buge a ka.” Inji daya daga cikin ‘yan kwamitin Mamman Sanusi Bukar.

Ya kara da cewa: ” Na biyu muka je muka nemo wasu da ake kira Police Scientific su ma suka kawo mana sakamakonsu cewa lallai dalibin makarantar Abdou Moumini, wanda ake kira Mala Bagale ba ya mutu ba ne don ya fadi da kansa bisa kan dutse.”

Kawo yanzu dai mahukuntan kasar ta Niger ba su ce komai game da wannan rahoton, amma wasu daliban da suka shaidi zaman bayyana sakamakon bincike da daren ranar Alhamis sun ce za su tashi tsaye domin nemo hakkin dan uwansu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1179total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.