Nigeria: Harin kunar bakin wake ya kashe mutane a Mubi

Rahotanni dai sun ce lamarin ya faru ne a wani masallaci da ake kira Masallacin Madina cikin garin na Mubi lokacin da ake sallar Asubah.

Akalla mutum 21 suka mutu bayan wani ya kai harin kunar bakin wake wani masallacin cikin garin Mubi da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni dai sun ce lamarin ya faru ne a wani masallaci da ake kira Masallacin Madina cikin garin na Mubi lokacin da ake sallar Asubah.

Dan kunar bakin waken yana tsakiyar jama’a ne lokacin da ya tayar da bam din shi bayan an tayar da Sallah.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga Sashen Hausa na BBC, kwamishinan watsa labarai na jihar Adamawa, Ahmed Sajo, ya ce hukumomi ba za su iya tabbatar da iya adadin wadanda suka mutu a harin ba tukunna.

Ya kara da cewa da yawa daga cikin mutanen da abin ya rutsa da su gabobin jikinsu sun tarwatse, saboda haka zai yi wuya a gane adadin su.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta tura ma’aikatan kiwon lafiya garin na Mubi domin yi wa wadanda lamarin ya shafa magani na gaggawa da kuma ceton rayuka.

Wannan ne karon farko da aka kai hari da ya kai haka muni garin na Mubi tun bayan sojojijn Najeriya sun kwato garin daga hannun ‘yan Boko Haram.

Mayakan Boko Haram dai sun kwace garin na Mubi ne a shekarar 2014, amman daga baya sojojin Najeriya suka kwato garin daga hannunsu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1651total visits,2visits today


Karanta:  Boko Haram: Shugabannin sojin Nigeria sun koma Maiduguri

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.