Nigeria: Hatsarin jirgin kasa ya kashe mutane a Lagos

A kalla mutum uku ne suka mutu bayan an yi hatsarin jirgin kasa a unguwar Agege da ke birnin Legas a kudancin Najeriya

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar jiragen kasa ta Najeriya da ke da hedikwata a Legas, Yakubu Mahmud, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wata motar tirela da take kokarin tsayawa ta daki jirgin kasan.

Jirgin dai ya taso ne daga yankin Ijoko zai tafi yankin Ido da suke cikin birnin Lagos din.

Jami’in ya ce wadanda suka rasa rayukansu suna cikin wadanda suka fado daga bakin kofar jirgin.

Wasu rahotanni na cewa akwai yiwuwar yawan wadanda suka mutu ya karu domin akwai mutane da dama da suka ji munanan raunuka.

Ba a dai cika samun hatsarin jirgin kasa a Najeriya ba kamar su Indiya inda aka fi amfani da layin dogon.

Asalin Labari:

BBC Hausa

457total visits,1visits today


Karanta:  An cafke mutane 24 da ake zargi 'Yan Boko Haram ne a Jihar Edo

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.