‘Nigeria na yin asarar $ 21bn saboda rashin shayar da nonon uwa’

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef, ya ce Najeriya na yin asarar $ 21bn saboda rashin shayar da nonon uwa.

Shugaban Asusun a Najeriya, Anthony Lake, ne ya bayyyana haka a wurin taro kan ‘makon shayar da nonon uwa’ a Abuja, babban birnin kasar.

A cewarsa, kudin da mata ke kashewa domin sayen madarar gwangwani da sauran abincin jarirai sun kai kashi 4.1 na kudin da kasar ke samu a duk shekara.

Ya kara da cewa, “Rashin shayar da jarirai nonon uwa ya sa mata na yin asara biyu: asarar rai da ta dama saboda shayarwar na kare yara daga cututtuka.”

Babban jami’in na Unicef ya ce, “bai wa jariri nonon uwa a wata shida na farko yana hana shi kamuwa da gudawa da ciwon hakarkari, cutuka biyu da suka fi kashe jarirai.

Kazalika, matan da ke shayar da jariransu na tsira daga kamuwa da ciwon daji na mama da mahaifa.”

Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware wannan makon don nuna muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zallah.

Yayin bukukuwan makon, an kaddamar da gamayyar kasa da kasa don ganin yadda za a wayar da kan mutane su gane muhimmancin shayar da jarirai.

MDD ta ce idan da za a zuba jarin dala 4.70 don shayar da duk jariri daya, to za a samu ribar dala miliyan 300 nan gaba wanda hakan zai habaka tattaln arzikin kasar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

500total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.