Nigeria ‘Ta Fita Daga Matsin Tattalin Arziki’

Wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics, NBS, ta fitar ya nuna cewa kasar ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta fada.

Rahoton ya ce tattalin arzikin ya bunkasa da kashi 0.55 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2017 idan aka kwatanta da rubu’i na biyu na shekarar 2016.

Hakan yana nufin cewa girman wannan bunkasa da aka samu ya haura wanda aka samu a rubu’i na biyu na shekarar 2016 da kashi 2.04 cikin 100.

Tattalin arzikin kasar ya samu wannan tagomashi ne bayan da ya kwashe rubu’i biyar yana ci gaba da tsukewa.

A lokacin da tattalin arzikin ya bunkasa, ana fitar da gangar danyen mai 1.84m a kowacce rana, in ji NBS.

Ta kara da cewa, baya ga man fetur, harkar noma da inshora da gas da lantarki na cikin abubuwan da suka taimaka wajen bunaksar tattalin arzikin.

Asalin Labari:

BBC Hausa

351total visits,2visits today


Karanta:  Buhari Ya Kaddamar da Kwamitin Duba Tsarin Albashin Ma’aikata

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.