Nigeria: Wane bangare Buhari zai fi kashe wa kudi a kasafin 2018?

Najeriya ta bayyana kasafin kudinta na 2018, wanda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke fatan zai samar da yanayin cigaba daga halin karayar tattalin arzikin da kasar take fama da shi.

Shugaba Buhari ya bayyana kasafin kudi na Naira tiriliyan 8.6 a gaban majalisar kasar, wanda ya ce zai samar da ayyukan yi ga matasa da kuma sabbin gine-gine a kasar.

A bana ne Najeriya ta fita daga matsalolin koma-bayan tattalin arziki a hukumance bayan faduwar farashin man fetur, a shekarun baya.

A jawabin da ya gabatar, shugaba Buhari ya ce Najeriya: “ba za ta yi sakacin komawa cikin rikice-rikicen da suka addabi kasar a shekarun baya a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ba.

Kasafin na bana ya zarce na bara da karin kaso 16 cikin 100 kuma gwamnatin Najeriya ta ce za ta mai da hankali wajen samar da hanyoyi da kiwon lafiya da gidaje da kuma samar da ayyukan yi.

Jadawalin manyan ma’aikatun da suka samu kaso ma fi yawa a wannnan kasafin kudin na 2018 ya nuna cewa ayyuka raya kasa ne ke kan gaba.

A karkashin kasafin kudin na bana, ma’aikatar Wutar Lantarki, Ayyuka da Gidaje ce ta sami kaso ma fi tsoka na Naira biliyan 555.88.

Shugaba Buhari ya bayyana dalilin ba wannan ma’aikata kaso mai yawa: “Gwamnati na son samar da sabbin ayyuka da za su kawo cigaban tattalin arziki da raya kasa.”

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ce ke ta biyu, inda aka ware mata Naira biliyan 510.87, daga nan sai ma’aikatar Ilimi da zata sami Naira biliyan 435.01.

Daga nan kuma sai ma’aikatar Tsaro da zata sami Naira biliyan 422.43, sai ma’aikatar Kiwon Lafiya da aka ware mata Naira biliyan 269.34.

Ma’akatar Sufuri an ware mata Naira biliyan 263.10, inda aka ba ma’aikatar Noma da Raya Karkara Naira biliyan 118.98.

Karanta:  Buhari ya kammala tsara kasafin kudin 2018

Sai kuma ma’aikatar Albarkatun Ruwa da za ta sami Naira biliyan 95.11, sai kuma ma’aikatar Ma’aikatu da Cinikayya da Zuba Jari mai kason Naira biliyan 82.92

Amma ana sa ran gibin dake tsakanin kasafin kudin shiga da ainihin wadanda za su shiga lalitar gwamnati zai ragu daga Naira tiriliyan 2.36 na kasafin kudin bara zuwa 2.005 a kasafin kudin bana.

Kasafin kudin dai zai zama doka ne kawai idan ‘yan majalisar kasar suka amince da shi.

Bangaren gwamnati da na majalisa sun sha kai ruwa rana kan kasafin kudi musamman wanda ya gabata, al’amarin da har ya kai ga tonon silili tsakanin ‘yan majalisar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

41316total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.