Nigeria: ‘Yan Sanda Uku Sun Mutu a Harin Gidan Zoo

A Najeriya 'yan sanda uku sun mutu a wani harin da wasu da ba a san su ba suka kai wa gidan zoo din Ogba da ke birnin Benin a jihar Edo.

Wata sanarwar da Ministan Yada Labaran kasar, Alhaji Lai Mohammed, ya fitar ta yi Allah-wadai da harin da aka kai ranar Lahadi, inda aka saci shugaban gidan namun dajin Dokta Andy Ehanire.

Mataimaki na musamman ga ministan, Segun Adeyemi, ya tura wata sanarwa ga manema labarai.

Wadda a cikinta ya ce harin da aka kai kan wani wurin ziyarar masu yawon bude ido zai jawo koma baya ga kokarin da gwamnatin kasar na farfado da harkar yawon bude ido.

Sanarwar ta ambato ministan yana cewa: ”Nasara ko kasawa na wuraren yawon bude ido ya dogara ne kan zaman lafiya.”

Ta kara da cewa irin wannan harin da aka kai gidan zoon ya saba wa yanayi na harkar yawon bude ido da kuma kokarin gwamnati na habaka fannin yawon bude idon a matsayin wata hanya ta ciyar da kasa gaba.

”Kashe ‘yan sanda uku da aka saka gidan zoon domin tabbatar da tsaro ga masu zuwa kallon dabbobi da sace shugaban gidan zoo din da kuma tashin hankalin da masu ziyara a gidan zoo din suka fuskanta lamari ne na bacin rai,” in ji ministan.

Alhaji Mohammed ya ce gwamnati za ta matsa kaimi wajen kara matakan tsaro a dukkan wuraren yawon bude ido, inda ya nemi wadanda suka sace Dokta Ehanire da su sake shi cikin gaggawa.

Ministan ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan ‘yan sandan da aka kashe a harin.

Asalin Labari:

BBC Hausa

516total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.