Nijar: Sama da Dabbobi 16,000 Sun Salwanta a Ambaliyar Ruwa

Ambaliyar ruwa a Nijar ta raba dubban mutane da gidajensu

Ofishin bada agajin jinkai na majalisar dinkin duniya OCHA, ya ce akalla mutane 54 ne suka rasa rayukansu, sakamakon iftila’in ambaliyar ruwan da aka samu a Jamhuriyar Nijar, yayinda sama da mutane 200,000 suka rasa matsugunnasu.

Ofishin majalisar dinkin duniyar ya kuma ce, mafi akasarin hasarar rayukan ya auku ne birnin Yamai, kuma a birnin kadai akalla gidaje 11,000 ne ambaliyar ruwan ta rusa.

Ofishin bada agajin jikkan na OCHA ya ce Ambaliyar ruwa ta kuma lalata fadin akalla kadada 12,000 na amfanin gona bayaga dabbobi 16,000 da suka salwanta.

Ambaliyar dai ta fi shafar Yamai, Dosso, Tllaberi, Maradi da kuma Zandar.

Asalin Labari:

RFI Hausa

645total visits,1visits today


Karanta:  Abinda ‘Yan Najeriya Ke So Buhari Ya Fara Tunkara

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.