Nijeriya Bata Bukatar Tallafi Daga Kasashen Wajen Saboda Kungiyar Masu Rajin Kafa Kasar Biafra Wato IPOB – Gwamnatin Tarayya

Ministan Kasashen Wajen Nijeriya, Mr Geoffrey Onyeama, yace kasar bata bukatar wani dauki daga kasashen wajen don takaice duk wata barazana daga Kungiyar Masu Rajin Kafa Kasar Biafra (IPOB)

A wata ganawa da manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinki Duniya dake New York ranar Jumma’a da yamma yace kasar zata iya da duk wata barazana da take fuskanta daga kungiyar.

“Kungiyar IPOB yanzu haka barazana ce ta cikin gida don haka Nigeriya bata bukatar gudunmowar kasashen waje don magance ta,” a fadar ministan.

Acewarsa, IPOB tanada banbanci da kungiyar ‘yan tada kayar baya ta Boko Haram wanda abun da suka saka a gaba shi ne kame daukacin iyakokin kasar da kuma kashe mutanen da basu jiba basu gani ba.

“Shugaban kasa ya shirya tsaf dan fadawa shugabannin duniya cewa abubuwan da ake bukata dan samar da farin ciki da zaman lafiyar kasa shi ne kyakykyawan shugabanci da karfin tattalin arziki.

”Idan zamu iya samarda ingantaccen tattalin arziki da kyakykyawan shugabanci ga mutanen mu, munyi imanin cewa zamu iya magance da yawa daga cikin matsalolinmu.

“Nijeriya kasa ce ta matasa, yawanci al’ummar kasar suna kasa da shekaru 35 haka kuma yawancinsu basu da wani katabus.

“Basuda wani katabus saboda kamfar tattalin arziki, shi yasa muke da matsalolin ‘yan ci rani

“Da yawa daga cikin matasan sun sami kansu cikin halin da suke ciki yanzu saboda rashin kyakykyawan shuganbanci shekaru da dama da suka wuce, haka nan wannan shi ya hana matasan samun damarmaki ta bangaren ilimi da ayyukanyi.

“Dan haka shugaban kasa yake ta kokarin sauya fasalin kasar don samar da ginshikan ingantaccen shuganbanci

Karanta:  Sarkin Musulmi Ya Jaddada Mahimancin Zaman Lafiya

“Saboda mutukar kana da kyakykyawan shugabanci  haka kuma arzikin da Allah ya horewa kasar ana iya kaishi inda yakamata ta fuskar cigaban kasa, zaka iya magance da dama daga cikin matsaloli.”

Yace ba kamar kungiyar IPOB ba, kungiyar ‘yan tada kayar baya ta Boko Haram ba barzana ce kawai ga cikin gida ba harma kasashen wajen, duba da yadda take da alaka da kungiyar ISIS ta kasar Siriya da Iraki

Ministan harkokin Kasashen wajen yace matsayin shugaba Muhammadu Buhari shi ne dole ne a girmama Kundin Tsarin Mulkin Kasar.

Yayi jan hankali cewa yanzu dimokaradiyyar kasar ke girma tana da bukatar ta balaga tayi karfi sosai don iya magance wasu daga cikin matsalolin dimokaradiyyar kasar.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

727total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.