Nijeriya Za Ta Cigaba Da Zama Kasa Daya Mai Manufa Guda…. – Sultan

Sokoto – Maigirma Sarkin Musulmi, Ahaji Sa’ad Abubakar ya roki ‘yan Nijeriya su zauna lafiya da kowa su kuma kauracewa duk wani abun da zai yi barazana ga zaman lafiyar da ke akwai tsakanin mabanbanta kabilu.

Sarkin musulmin yayi wannan  kiran a wata sanarwa da Sakataren Majalisar Daular, Alhaji Umar Ladan ya fitar ranar Jumma’a a Sokoto

Abubakar yayi kira ga shugabannin al’umma da manyan mutane da su cigaba da kiran zaman lafiya a kasa ta hanyar ilimantar da matasa ba tare da duba ga banbance-banbancen al’adu dake akwai ba.
“Najeriya zata cigaba da zama kasa daya kan manufofin cigaba, baza mu bari ayyukan wasu baragurbi daga cikin mu ya raba kasar nan bangare-bangare ba.

“Haka kuma dole wadannan baragurbin a kirasu zuwa ga doka da oda ta hanyar manyansu da shugabannisu don su dakata da wadancan munanan dabi’un nasu,” Kamar yadda Abubakar din yayi gargadi.
Sarkin musulmin yace shugabannin gargajiya a kasa na iya bakin kokarinsu don kawo karshen halin da ake ciki yanzu inda ya bukacesu dasu ninka kokarin nasu.

“Ubangijin da ya hada mabanbanta kabilu masu mabanbanta addini da kyawawan al’adu cikin yalwataccen arziki su zauna tare su samar da kasa daya don haka zai kare kasar da mulkinta.

Ya yabawa Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro bisa kokarinsu na dawwamar da zaman lafiya dama cigaban kasar.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard

1250total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.