Osinbajo ya fidda sabbin Manyan Sakatarori 21 na tarayya

A Jiya mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya yadda da daukar ma’aikata guda 21 a matsayin Manyan Sakatarorin na gwamnatin tarayya. An dauki ma’aikatan ne bayan gudanar da jarrabawar tantancewa ta daraktocin tarayya. Sakatorotin sun hada da Umaru Muhammad Bello, Akpan Edet Sunday, Adeyibi Biola Adekunle, Aduda Gabriel Tanimu, Folayan Ayodele Olaniyi, Nabasu Bitrus Bako, Abdulahi Abdullazeez Mashi, Mu’azu Abdulkadir, Alibo Leon, Ehuria Georgina Ekeoma, Anagbogulfeoma Nkiruka, Walson Jack Didi Esther, Gekpe Grace Isu, Uwaifo Clement,Osuji Ndubuisi, Sulaiman Mustafa Lawal, Ibrahim Musa, Wen Odesola Olusade, Samsom Olaide and Ekaro Comfort Chukwuebobo.

An dauki ma’aikata da yawansu ya fara da daraktoci 300, wadanda suka zauna jarrabawa amma 78 suka tsallake aka zubar da 222. An sake gabatar da 78 din, inda su ka sake yin jarrabawar ta amfani da na’ura mai kwakwalwa wanda a ciki a ka dauki 59.

Asalin Labari:

dailyTrust, Muryar Arewa

460total visits,1visits today


Karanta:  Ethiopian Airlines na son karbe iko da Arik Air

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.