PDP: Magoya bayan Sheriff suna shawarar barin jam’iyya a Edo

Magoya bayan tsohon shugaban jam’iyyar adawa a Nageriya, PDP, Sanata Ali Madu Shariff a jihar Edo sun bayyana cewar basu da wani zabi illa su bar jam’iyyar idan bangaren shugaban jam’iyyar Sanata Ahmad Makarfi ya cigaba da yunkurin da yake yi na yin yafiya ga magoya bayan tsohon shugaban.

Dan majalisar wakilai ta kasa, Ehiozuwa Johnson Agbonnayinma ya bayyanar da hakan inda yake cewa kuskure ne a kalli magoya bayan Sanata Shariff a matsayin wadanda za’ayi wa yafiya, tunda ba su kasance yan ta’adda ba.

Da yake magana a jiya, Agbonnayinma ya kara da cewa abinda Sanata Shariff yayi ya nuna cewa ya yi ne a matsayin sadaukarwa ga jam’iyyar ta PDP, don haka bai kamata ayi masa kallon dan ta’adda ba.

Yace an roki Sanata Shariff daya taimaka wajen ceto jam’iyyar PDP a lokacin ta take neman mai taimakon ta inda kuma yayi iya bakin kokarin sa, wanda a yanzu ake ikiririn cewa za’ayi masa yafiya.

Ehiozuwa Johnson Agbonnayinma ya bayyanar da cewar bai san mai gobe zata haifar ba akan sa da kuma sauran magoya bayan Shariff.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

622total visits,1visits today


Karanta:  PDP: 'An tsawwala kudin fom din zabe a Kebbi'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.