PDP Ta Kafa Kwamitin Tsawaita Shugabancin Makarfi

Jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Sanata Ahmed Makarfi ta ce nasarar da Makarfi ya yi a Kotun Koli za ta ba shi karfin hada kawunan 'yan jam'iyya don tinkarar APC mai mulki a zabe na gaba.

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta kafa wani kwamiti wanda zai shirya babban taron jam’iyyar, inda ake sa ran duba yadda za a tsawaita shugabancin Sanata Ahmed Makarfi, wanda ya yi nasara kan bangaren Sanata Ali Madu Sheriff a Kotun Kolin Najeriya.

Kwamitin, wanda Gwamna Ifeanyi Okowa na jahar Delta da tsohon Gwamnan jahar Jigawa Sule Lamido ke jagoranta, zai kara wa’adin Makarfin ne bisa ga tanajin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Wani jigon jam’iyyar, Alhaji Faruk Ahmed Gusau, ya ce wannan karon za su bai wa jam’iyya mai mulki APC mamaki. Ya na mai ikirarin cewa PDP ta girmi APC kuma ta fi ta sanin siyasa. Shugaban jam’iyyar na Yankin Arewa Maso Yamma, Ibrahim Kazaure, ya yi kira ga bangaren Madu Sherif da su ka kaurace ma jam’iyyar da su zo a hade saboda a kudu tare a tsira tare.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar sun ce wannan mataki da jam’iyyar ta dauka na iya kaita ga nasara a zabe mai zuwa. Alhaji Abdullahi Jalo da Inuwa Garba sun ce rashin ayyukan yi da sauran matsaloli za su sa jam’iyya PDP ta yi nasara a zabe mai zuwa.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1041total visits,1visits today


Karanta:  Yemi Osinbajo ya yi 'kyakkyawar' ganawa da Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.