Rarara ya shiga hannun Hukumar Custom da laifin fasakwauri

Mawaki Dauda Kahutu Rarara Ya Shiga Hannun Jami'an Hukumar Hana Fasa Kwaurin Nigeria.

Jami’an kwastam na Najeriya sun kwace wadansu manyan motoci mallakar mawakin jam’iyyar APC Dauda Kahutu (Rarara) da yake aikin sumogal dinsu ta kan iyakokin da aka haramta a tsakanin Najeriya da kasar Benin da Jamhuriyar Nijar.

Rahotannin farko-farko sunce an kame motocin ne kirar Fijo-Fijo da Toyota-Toyota a jihohin Zamfara da Sakwato kuma aka  kawo su Kaduna.

Wasu gwamnonin APC guda uku suna ta ban baki ga shugaban kwastam Hamidu Ali cewa kayan dan jam’iyya ne, don haka a rufe  maganar a sallamesu.

Kwastam dai suna kama kayan marasa galihu su rike daga karshe su yi gwanjonsu, kuma babu wanda ya isa ya samu alfarma.

Asalin Labari:

Hausa Media

1686total visits,1visits today


Karanta:  Jam'iyyar APC ta Lashe Zabukan Jihar Legas

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.